Advertisement
Labaran Hausa

Mahaifan Yarinyar Yar Shekaru Uku Da Akayiwa Fyade Har Ta Mutu Sun Mika Sako Zuwa Ga Gwamnati

Mahaifan Yarinyar Yar Shekaru Uku Da Akayiwa Fyade Har Ta Mutu Sun Mika Sako Zuwa Ga Gwamnati

Iyayen yarinya nan ƴar shekara 3, Khadijah Adam, da ake zargin makwabcinsu, Baba Idi mai shekaru 49 da haihuwa ya yi wa fyade a ranar Litinin din da ta gabata, sun bukaci a yi musu adalci.

Iyayen na Khadijah, wacce a ka fi sani da Yasmin, sun yi zargin cewa fyaɗen ne ga sanya ƴar ta su ta rasu sakamakon bugun zuciya.

Mahaifin marigayiyar, Muhammad Adam, a wata tattaunawa da manema labarai a gidansa a jiya Litinin ya bukaci a yi masa adalci.

A na zargin Idi, mazaunin Lungun Haliru Mai Ruwa, unguwar Gama da ke Ƙaramar Hukumar, Nassarawa a Kano, ya aikata laifin ne a ranar Litinin, Satumba, 26, 2022.

“Wannan wani abu ne na cin amana ga makwabci ya aikata wannan aika-aika. Abin da nake bukata shi ne adalci,” in ji Adamu.

Masu sauraranmu a Koda yaushe bayan Kun karanta wannan labarin zamu so karben a sahen mu na tsokaci.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button