Advertisement
Labaran Hausa

Mai albashin 30k bazai ina rike iyalinsa ba mai dubu 50k ma maleji yake, cewar Jamila Ibrashim

Mai albashin 30k bazai ina rike iyalinsa ba mai dubu 50k ma maleji yake, cewar Jamila Ibrashim

Jamila Ibrahim ta bara inda ta bayyana cewa, idan dai lallai albashin naira dubu talatin 30k kake samu a wata to lallai bazai iya rike maka mata ba.

Jamila dai itace matar dake da dandalin Home of Solace Extensions a sahar Facebook.

Jamila ta bayyana hakan ne a wani rubutu data wallafa a shafin ta na facebook, Jamila ta kara da cewar mai karbar albashin naira dubu hamsin 50k ma maleji yake yi a wata, ballantana kuma wanda yake karbar naira dubu talatin.

Idan kana karban dunu talatin 30k a matsayin albashi to ka dage da neman wata sana’a domin dubu talatin 30k sam sam koda Kaine sarkin maneji ta duk duniya bazai isheka rike mata ba, mai karban dubu hamsin ma maneji yake bare kai.

Ta kara da cewa, wasu matasan don takamar cewa suna yin aikin koyarwa a makarantu masu zaman kansu, ko kuma suna karkashin shirin gwamnatin tarayya na “N-Power” ana basu dubu talatin a wata, sai ya zamto sun kwanta ba tare da tashin domin neman karin hanyoyin samun kudin shiga ba.

Tace, wasu gani suke wannan dubu talatin da ake basu ta ishe su komai da komai.

Amma basu san cewa, ba haka bane sai a lokacin da wata gagarumar hidima ta fado musu, kamar hidimar haihuwa da makamantan su.

Sai matarka ta haihu zaka gane dawainiyar yau da kullun ya wuce maganar albashin dubu talatin 30k, dole matasa su fadada hanyar nema.

Jamila Ibrahim ta bayarda da shawarar cewa, dole ne fa matasa su tashi tsaye wajen fadada hanyar nema don samu su tsira da mutuncin su ba wai su dogara kacokan kan dan albashin da ake basu ba.

Dole fa sai an fadada nema, a rubutun nan gaba zanyi magana akan sana’a mai kyau wanda namiji zai yi ba tare da wani jari mai yawa ba kuma a kullun zai iya samin dubu biyar zuwa ashirin a rana.

In har mutum bai da girman kai to lallai za’a dace dan da yawa a nan Abuja naga suna sana’ar kuma ya karbe su.

Sai dai kuma wasu mabiyan ta a shafin nata sunyi mata martani kan cewar albashin dubu talatin ko kasa da haka ma zai iya rike magidanci da shi da iyalin shi suci su sha suyi walwala.

Wani mai suna Shamsuden Sa’id Mu’az yayi martani da cewa, albashin kasa da dubu talatin ma yana iya rike wasu dasu da iyalan su cikin walwala.

To Wanda Kuma nanne hanyar samun nasa fa, wani koyarwar itace sana’ar sa sannan maganar dubu talatin 30K ba zata rike mata ba kin dai fada ne kawai wasu ma basu kai dubu talatin 30K din ba, amma suna rike da iyalin su cikin kwanciyar hankali da rufin asiri.

Dubu talatin 8k nake kwasa a kowane wata, kuma haka muke rayuwa cikin jin dadi da walwala.

Wadatar abu tafi yawan shi, Allah yasa ma al’amurran mu albarka, inji Salmanu Shehu Bagida.

Muktar Abubakar kuma cewa yay: Almost dubu talatin 30k nake kashewa a utilities kawai a wata, indai dubu talatin 30k ne earnings din mutum a wata to abun tausayi ne gaskia.

Rahoto daga👉 Labarun Hausa

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button