Advertisement
Labaran Hausa

Mai Yayi Tsafi: Yadda Matar Aure Ta Shawarchi Mijinta Da Ya Kara Mata Kishiyoyi Bayan Ta Kasa Haihuwa

Mai Yayi Tsafi: Yadda Matar Aure Ta Shawarchi Mijinta Da Ya Kara Mata Kishiyoyi Bayan Ta Kasa Haihuwa

Wata matar aure mai suna Nerimima Juma, ‘yar kasar Uganda wacce ta ba mijinta shawarar ya kara auro wasu matan ta zama abin magana a yanar gizo.

Nerimima ta bayyana cewa bata da wata matsala da yin kishi da wasu matan akan mijinta Asanasi Mulingomusindi.

A wani bidiyo da ta tashar Afrimax English ta saka a YouTube, matar auren ta kasa samun ciki tun bayan auren su da mijin na ta. Jaridar Legit.ng ta rahoto.

Domin magance matsalar, Nerimina ta shawarci mijinta ya karo aure domin samun wacce za ta haifa masa ‘ya’ya.

Asanasi ya dauki shawarar matar ta sa, inda ya kara auren wata matar wacce yanzu har ta haifa masa yara bakwai.

Abin ban sha’awar shine, bayan zuwan matar ta biyun, matar sa ta farko ita ma ta fara samun juna biyu wanda yanzu har ta haifi yara hudu.

Iyalan sun yi amanna cewa zuwan mace ta biyun ne ya bude hanyar su ta samun haihuwa.

Mutumin yanzu haka ya kara auren wata matar, inda yawan matansa ya zama guda uku yanzu.

masu sauraranmu a Koda yaushe bayan Kun karanta wannan labarin zamu so karben a sahen mu na tsokaci.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button