Labaran Hausa

Malam Muhammad Sulaiman mai tarin ‘yaya 18 da Mata 3 ya kara haihuwar ‘yar mace tare da kara aren Mata cikon ta 4

Malam Muhammad Sulaiman mai tarin 'yaya 18 da Mata 3 ya kara haihuwar 'yar mace tare da kara aren Mata cikon ta 4

Malam Muhammad Sulaiman, malamin
kwalejin ilimi mai tarin iyali da yara uku ya
bayyana cewa, ya samu karuwa.

Mai tarin iyalin ya sanar da cewa, a ranar daya aurar da diyarsa ne ya auro matarsa ta hudu duk a ranar Mahaifin yaran 18 a baya ya sanar da cewa, yanzu ya zama mai yara 19 da mata hudu cif inda ya rufe kofa gaba daya.

Malamin makarantan nan mai tarin iyalai da mata uku mai suna Malam Sulaiman Muhammad, ya haifa ‘Da na 19 inda ya bayyana hotunan a shafin sa na Facebook.

Kamar yadda mahaifin yara 19 din mai mata uku ya bayyana ya sanar da cewa, ya auri mata ta hudu inda ya rufe kofa da ita.

Har ila yau, Muhammad Sulaiman ya bayyana yadda ya aurar da diyarsa daya inda a rana daya ya auro mata ta hudu tare da samun karuwar yaro na cikon 19.

Rahoto daga👉 Legit.ng hausa

A wani labari na daban.

Gwamnatin Buhari ta Maka kamfanin Sadarwar zamani Meta ( Facebook) Kotu tare da Neman A Biyata Naira Biliyan Talatin..

Gwamnatin tarayyar Najeriya ta shigar da kamfanin Meta Platforms Incorporated a kotu a Abuja tana neman a biya ta N30bn..

Hukumar kula da tallace-tallace a Najeriya, ARCON, ta ce ta shigar da ƙara kan kamfanin Meta Platforms Incorporated (masu Facebook, Instagram da WhatsApp) da wakilin ta AT3 Resources Limited a babban kotun tarayya ta Abuja…

A cewar sanarwar da hukumar ta fitar a yau Talata, 04/09/2022 ARCON na neman kotun ta tabbatar da cewa cigaba da yi wa yan Najeriya talla ba tare da hukumar ta tantance tallar ba ya saba dokar Najeriya, kuma haramun ne…

Daga Ƙarshe ARCON ta bayyana cewa wannan tallace tallace da akeyiwa Ƴan Najeriya batare da izini ba yana jawowa Najeriya Asarar Maƙudan Kuɗaɗe.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button