Advertisement
Labaran Hausa

Martanin wani malami akan mutuwar Kamal Aboki wanda hakan bai yiwa wasu dadi ba

Martanin wani malami akan mutuwar Kamal Aboki wanda hakan bai yiwa wasu dadi ba

Ananan ana cigaba da jimamin mutuwar shahararren dan wasan barkwanci Kamal Aboki, wanda ya rasu ranar Litini 16 Ga watan daya sanadiyyar hadarin mota data rutsa dashi daga Maiduguri zuwa Kano.

Majiyarmu ta samu wannan labarin daga shafin “Hausaloaded” inda mutane suke ganin abinda malamin ya fadi bai dace ba sai dai ita daman gaskiya daci ne da ita.

Mutuwar Kamal din ya jijjiga mutane da dama inda jaruman Tiktok suka dinga kuka kan rashin na abokin nasu, Kamal din yana kan samun shaida na gari daga bangarori da dama.

Sani Malami ya fitar da wani bidiyo inda yace duk wani da yake kirkirar labaran karya domin yasa mutane nishadi Ko dariya Comedy bashi ba rahamar Allah, inda Malamin ya karanto Hadisi.

Zaku iya kallon bidiyon dake kasa domin kuji abin da Malamin yake fada duk da kuwa yasha suka a waja jama’a.

Ga bidiyon a kasa domin ku kalla.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button