Advertisement
Labaran Hausa

Masha Allah Jarumar Kannywood Halima Atete Zata Shiga Daga Daka A Satinnan

Masha Allah Jarumar Kannywood Halima Atete Zata Shiga Daga Daka A Satinnan

Aure lokaci a karshen satinnan da yardar mai duka za’a daura auren Fitacciyar jaruma Halima Atete da Angon ta mai suna Muhammed Kalah wamda za’a daura a ranar Asabar dinnan mai zuwa a masallacin juma’ar dake Abuja sheraton new bustop dake maidugurin jahar Borno Da Misalin karfe goma na safiya

Abokin Aikin ta Darakta Saddiq mafiya ne ya wallafa katin gayyatar daurin auren tare da yi mata fatan AIkhairi

Tun bayan auren jaruma Ruqayya Dawayya dama ake kishin kishin din Jaruma Halima Atete ce ke kan layi wanda aka bayyana itama kwanannan za’a sha bikin ta kamar yadda shafin labaran kannywood dake dandalin Twitter Suka bayyana sai gashi kuwa Allah ya kawo mu lokaci

Sau da dama an sha yada labarin auren jaruma sai zancen ya zama kanzon kurege wanda a shekarun baya har hotunan jarumar aKa dinga yadawa da wani dan kasuwar cd a kofar wambai mai suna Musa Best seller ana Sa ran auren nasu sai dai daga bisani aka fahimci ba haka zancen yake ba

Dama hausawa na cewa komai lokaci sai a wannan karon Allah ya kawo lokacin auren jarumar da fatan Allah yasa abokin zamane bada zaman láfiya ameen

https://www.instagram.com/p/ClMXRGvIcM7/?igshid=YmMyMTA2M2Y=

Masu sauraranmu a Koda yaushe bayan Kun karanta wannan labarin zamu so karben a sahen mu na tsokaci.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button