Advertisement
Labaran Hausa

Masha Allah Jinin Sarauta : Dan Sarkin Kano Yana Shirin Yin Wuff Da Diyar Sarkin Bichi

Masha Allah Jinin Sarauta : Dan Sarkin Kano Yana Shirin Yin Wuff Da Diyar Sarkin Bichi

Kano – Labari mai zafi dake zuwa a safiyar yau Lahadi shi ne na shirin shagalin auren jinin sarauta biyu da kuma zumunci, wanda za a yi a Kanon dabo.

Kyakyawan matashi mai kasaita, Yarima Sanusi Aminu Bayero zai angwance da zukekiyar budurwa mai aji, Gimbiya Ummi Nasir Bayero.

Yarima Sanusi Aminu Bayero ‘da ne wurin Mai Martaba, Alhaji Aminu Ado Bayero, sarkin Kanon Dabo.

Ita kuwa Gimbiya Ummi Nasir Bayero, yar kwalisa, diya ce ga Mai Martaba, Alhaji Nasir Ado Bayero, sarkin Bichi kuma sirikin shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Kamar yadda aka sani, bayan auren jinin sarauta zalla da wannan shagalin zai kasance, aure ne na dangi da zumunci tunda Mai Martaba Sarki Kano, Aminu Bayero, da Mai Martaba Sarkin Bichi, Nasir Ado Bayero, mahaifinsu da mahaifiyarsu daya.

Kalli Wallafawar Anan

“Wani auren jinin sarauta, kuma ‘dan wa da yar kani ne auren. Yarima Sanusi Ado zai auri Ummi Nasir Ado Bayero. Mun kosa.”

Masu sauraranmu a Koda yaushe bayan Kun karanta wannan labarin zamu so karben a sahen mu na tsokaci.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button