
Masha Allah Yadda Aka Gudanar Da Bikin Jaruma Saratu Zazzau Wato Dr Girema A Shirin Kwana Casain
Masha Allah Yadda Aka Gudanar Da Bikin Jaruma Saratu Zazzau Wato Dr Girema A Shirin Kwana Casain
Kamar Yadda Kuka Sani Mafi Akasarin Jarumar Kannywood Mata Sun Fara Yin Aure Domin Ibadar Allah Amma Mafi Rinjaye Daga Cikinsu Suna Gudanar Dashi Cikin Sirri Ne
Hakan Ne Ya Faru Ba Zato Ba Tsammani Sai Jin Labarin Auren Jarumar Shirin Kwana Casa’in Aka Wato Saratu Zazzau Kamar Yadda Shafin Labaran Hausa Suka Wallafa
‘Saratu Zazzau, fitacciyar jarumar Kannywood wacce ta fito a fim din Kwana Casa’in mai dogon zango a Dr. Girema ta yi aurenta jiya, ranar Juma’a, 14 ga watan Octoban 2022.
Jarumar ta amarce da angonta, wanda su ka kwashe lokaci mai tsawo su na soyayya wanda sai yanzu Allah yayi za su yi aure.
Sanin kowa ne cewa jarumar ta dade tana fim, sai dai bata shahara sosai ba sai a wannan karon da ta dauki roll mai kyau a Kwana Casa’in inda tayi farin jini kwarai bayan bayyana a shugabar wata makaranta.
A kwanakin baya BBC ta zanta da ita inda ta shawarci matan da basu shiga fim ba da su dakata, kada su shiga, su je suyi karatunsu sannan suyi aure.
Ta kuma bayyana dalilin da ya sanya auren ‘yan fim ba ya karko, inda tace akwai mazan da ke kallonsu a talabijin amma kuma niyyarsu akansu ba mai kyau bace. Wannan ya sanya da zarar sun auresu, babu jimawa sai su sake su.
Auren da tayi jiya ya bai wa kowa mamaki, sai dai wakilin Labarun Hausa ya samu nasarar samun rahotanni har da hotuna ta hannun Zainab Baba Ahmed, wacce itama ta halarci bikin inda tace abu ya yi armashi.
Muna mata fatan alkhairi tare da addu’ar Allah yasa mutu ka raba. Ameen’
Masu sauraranmu a Koda yaushe bayan Kun karanta wannan labarin zamu so karben a sahen mu na tsokaci.