Advertisement
Labaran Hausa

Masu zargin ina saka kalmomin batsa a cikin wakokina su daina, cewar Kawu Dan Sarki

Masu zargin ina saka kalmomin batsa a cikin wakokina su daina, cewar Kawu Dan Sarki

Matashin mawaki na masana’antar Kannywood “Muhammad Khalid” wanda aka fi sani da Kawu “Dan Sarki”,  yana daya daga cikin mawakan wannan zamani da tauraruwar su take haskawa.

Kawu Dan Sarki yayi fice ne tun da ya saki wata wakar sa mai suna “Ingallo” wanda tayi suna sosai a soshiyal midiya.

A Kwanan nan Kawu Dan Sarki yayi hira da mujallar Fim inda ya ba da tarihin sa da dalilin sa na shiga harkar waka, da sauran su, kamar haka:

Mujallar FIM ta bukaci Kawu Dan Sarki ya fada musu tarihin rayuwar ka, inda ya fara da cewa:

Suna na Muhammad Khalid amma anfi sani na da Kawu Dan Sarki ina da kimanin shekaru ashirin da takwas 28 a duniya, ni haifaffen jihar Bauchi ne kuma dukkan karatu na a jihar Bauchi na yi amma iyakaci na sakandire ne.

Ni kafinta ne sai dai yanayin jiki na bai bani damar in iya yin wani aikin karfi ba, idan na fita sana’ar kafinta a rana ina samun kudin da ba sukai dubu diyu ba 2000 ba, kuma kudin a wurin magani su ke karewa wasu lokutan ma sai anyi ciko a gida.

Mujallar Fim ta sake tambayar Kawu Dan Sarki cewa, ya aka yi ka fara waka, inda shi kuma ya fara basu amsa da cewa:

Sanadin fara waka ta shi ne neman kudi, kamar yadda na fadi ba zan iya aikin karfiba abin dai da yawa, amma dai a takaice ni abin da ya kai ni situdiyo ba waka ba ce neman kudi na je.

Sabida ina aikin karfi aikin kafinta in samu dubu daya amma ta kare a magani harma a kara da ciko a gida, wannan shi yasa na koma situdiyo in samu naira dari dari biyu a cikin inuwa.

Mujallar Fim ta sake tambayar Kawu Dan Sarki kan cewa, yaushe ya fara waka, insa shi kuma yace musu: Ban share wasu shekaru masu yawa a harkar waka ba.

Bayan haka sun sake tambayar sa da cewa, mai yasa kake amfani da kalmomin batsa a wakokin ka, inda shi kuma yace:

Masu zargin ina saka kalmomin batsa a cikin wakoki na su daina, kawai dai ina zurfafa kalamai ne sabida suyi kwari a cikin wakoki na.

Mujallar Fim suka sake masa tambaya da cewa, wadanne irin wakoki ka fi yi, inda shi kuma yace:

Yanayin wakoki na kala daban-daban ne,  ina na soyayya, suna, biki, siyasa da sauran su, amma dai nafi karkata ga wakokin soyayya.

An sake masa tambaya da cewa, wace wakar kace fitacciya wacce kowa ya san ta, sai Kawu Dan Sarki yace: Wakar Ingallo Na Ciwo.

Mujallar Fim FIM: Wanene ubangidan ka a harkar waka?DAN SARKI: Mawaki Dauda Kahutu Rarara neubangida na a Kannywood, saboda shi ya daukinauyin bidiyon mafi yawan wakoki na har duniyata san ni.

Zaku iya kallon bidiyin dake kasa domin kuji cikekkiyar shirar da aka yi da Mawaki Kawu Dan Sarki.

Ga bidiyon a kasa domin ku kalla.

 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button