Advertisement
Labaran Hausa

Mata Yadda Zaku Magance Kanka Daga Sankarar Mama Maganin Yana Tartare Ga Mazajenku

Mata Yadda Zaku Magance Kanka Daga Sankarar Mama Maganin Yana Tartare Ga Mazajenku

Kwararriya a bangaren lafiya kuma shugaban cibiyar Lafiya ta Chartma Herbal Health Centre ta bukaci maza su rika shan mama a cikin watan Oktoba a wani mataki na wayar da kai game da kansar mama.

An ware watan Okotoban kowace shekara a matsayin watan wayar da kai kan cutar sankarar mama a faɗin duniya.

Charity Twumasi Ankrah a hirar da ta yi da KMJ a shirin Prime Morning a ranar Talata ta yi bayanin cewa shan mama na taimakawa rage wa mata kamuwa da kansar mama.

A cewarta, yana da muhimmanci ga mace ya zamana ana shan mamanta don yana kara lafiya. Ta ce:”Shayar da yaran ku mama yana da matukar muhimmanci. Shi yasa idan mace bata haihu ba, abin damuwa ne, akwai damuwa don akwai amfani a shayarwa.

” Kwararriyar ta kara da kira ga maza wadanda ba su yin hakan a baya su daure su ko na wannan watan ne domin matansu su amfana a yayin da ake bikin watan wayar da kai game da kansar nono.

Hakazalika, kwararriyar a bangaren lafiya ta nuna cewa ba wai kullum bane ake bukatar haka, sai dai lokaci zuwa lokaci. Ta kuma gargadi maza su dena yamutsawa matansu mama don hakan na iya musu ciwo, tana mai cewa ba ‘balan-balan bane’.

Charity Ankrah ta kuma shawarci mata wadanda suka kamu da kansa su yanke nonon da ya kamu don kare sauran jikinsu. Ta ce hakan ba karshen rayuwa bane.

Ta ce: “Kamuwa da kansar mama ba karshen rayuwa bane. Ya kamata in iya cire wanda ya kamu don ceton rayuwa na. Ba zai yi dadi in cire dukkan biyun ba, amma zan iya cire daya.

” Ta kuma shawarci mata su cire kunya su rika zuwa asibiti don a tantance su idan kuma ta kama a cire su daure a yi hakan.

Kwararriyar ta kuma yi kira ga al’umma su dena tsangwamar matar da aka yanke wa mama saboda kansa.

Daga karshe ta shawarci mata su tafi asibiti mafi kusa da su a cikin watan Oktoban a duba su a yayin da ake bikin wayar da kan na kansar nono.

Masu sauraranmu a Koda yaushe bayan Kun karanta wannan jawabin zamu so karben a sahen mu na tsokaci.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button