Advertisement
Labaran Hausa

Matar aure ta bayyana dalilin da yasa ta amincewa direbanta yake lalata da ita har suka haifi ‘yaya biyu

Matar aure ta bayyana dalilin da yasa ta amincewa direbanta yake lalata da ita har suka haifi 'yaya biyu

Wata matar aure ‘yar kasar Ghana ta bayyana yadda taci amanar mijinta da direbanta, wanda yanzu shine uban ‘yayanta.

Bayan ta kasa samun sukuni bisa abinda ta aikata, matar auren ta tonawa kan ta asiri inda ta bayyana yadda ta samu juna biyu sau biyu tare da direbanta.

Da take bayyana abinda ya faru, matar auren wacce aka sakaya sunan ta tace, aurenta da mijinta ya kai sheka rashida amma bata samu juna biyu ba, kamar yadda “Labarun Hausa” suka ruwauto.

Ta yanke shawarar zuwa ganin likita wanda yayi mata gwaje-gwaje inda ya gaya mata cewa babu wata matsala a tattare da ita, sai dai mijinta yaki zuwa domin a duba lafiyar sa.

Da take cigaba da bayar da labarin nata mai matukar kaduwa, matar auren ta bayyana cewa sai ta fara sakarwa direbanta fuska wanda ta bayyana a matsayin mutumin kirki.

Bayan alaka ta kullu a tsakanin su, sai suka bige da yin lalata da juna inda har ta samu ciki, bayan ta haifi yaron farko, ta kara samun wani juna biyun tare da direban.

Matar auren ta bayyana cewa, direban ya san cewa yaran guda biyu na shine, sai dai a daya bangaren kuma mijinta bai san cewa yaran ba na shi bane.

Rahoto daga👉 Labarun Hausa

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button