
Labaran Hausa
Mawakin kannywood Abdul D One ya nuna alhininsa kan rasuwar dan wasan barkwanci Kamal Aboki
Mawakin kannywood Abdul D One ya nuna alhininsa kan rasuwar dan wasan barkwanci Kamal Aboki
Shima mawakin masana’antar kannywood Abdul D One ya nuna alhinin rasuwar dan wasan barkwanci Kamal Aboki, inda yayi wata wallafa a shafinsa na Instagram kamar haka.
Innalilahi wa Inna ilahirraji’un Allah
Yasa Cen Yafi Nan Kamal Ina Rokon Allah Yasadaka Da Babban Masoyi Annabi Muhammad SAW.
Mabiyan Abdul D One sunyi addu’a sosai ga marigayin Kamal Aboki a sasgen tsokaci, inda suka yi ta nema masa gafara Ubangiji.
Muna rokon Allah ya jikansa ya gafarta masa kurakuransa, yasa Aljannah ce makomarsa.