Advertisement
Labaran Hausa

Mawakiya Ummi B.Y ta maka mawaki El-Mu’az Birniwa a kotu kan yi mata barazanar zai sa a kashe ta

Mawakiya Ummi B.Y ta maka mawaki El-Mu'az Birniwa a kotu kan yi mata barazanar zai sa a kashe ta

Mawakiya kuma jaruma a masana’antar Kannywood “Amina Abdullahi” wadda aka fi sani da Ummi B.Y., ta maka fitaccen mawakin nan El-Mu’az Muhammad Birniwa a kotu kan zargin tsoratarwa, kamar yadda “Fim Magazine” suka ruwaito.

Ta shigar da karar ne a babbar Kotun Majistare dake unguwar Rigachikun a Kaduna a ranar 29 ga watan Satumba 2022, ta hanyar lauyan ta “Abdulsaleem Umar na cambar M.T. Mohammed and Co. (Pinnacle Chambers)’ dake titin Alkali cikin garin Kaduna.

Sammacin karar wanda mujallar Fim ta samu kwafen sa ya nuna cewa, Ummi ta yi karar El-Mu’az ne bisa babban laifin barazana (direct criminal complaint for the offence ofintimidation), wanda ya saba wa sashe na 377 na kundin final kod na jihar Kaduna na shekarar 2017.

A sammacin, jarumar ta fada wa kotun cewa ita mazauniyar garin Birnin Yero ce yayin da shi El-Mu’az mazaunin Unguwar Kaji ne dake garin Kaduna, don haka kotun na da hurumin sauraren karar.

Tace, a ranar 2 ga watan Satumba 2022 ta kira wanda take karar a waya domin su gaisa a matsayinsa na abokin huldar ta, amma sai kawai ya shiga surfa mata zagi tare da yi mata barazanar sai ya sa yaran sa sun kashe ta kuma babu abinda za’a yi tunda yana da iko a cikin a’umma.

Ta kara da cewa, a cigaba da barazanar da yayi mata da misalin karfe 9 na dare a ranar 22 ga watan Satumba sai ga wasu ‘yan daba ya turo mata har gida domin su dauke ta su tafi da ita zuwa wani waje da bata sani ba, amma wasu bayin Allah suka taimaka mata suka hana ‘yan iskan shiga gidan.

Yanzu wadda ke karar ta na fargabar fita daga gida sabida tsoron kada wanda ake karar ko yaran sa da ya dauka su kai mata hari ba tare da wani dalili ba, cewar inji lauyan ta.

Yace, a yanzu haka El-Mu’az ya na nan yana neman Ummin ruwa a jallo a kan tunanin cewar shi wani isasshe ne wanda kome ya aikata baza a iya yi masa komai ba.

Lauyan ya nuna wa kotun cewa, wannan abu da ake zargin El-Mu’az da aikatawa babban laifi ne wanda ya saba wa sashe na 377 na kundin finalkod na jihar Kaduna na shekarar 2017.

Rahoto daga👉 Fim Magazine

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button