Advertisement
Labaran Hausa

Mijina ya sakeni amma bai bani takardar shika ba cewar Amaryar Tiktok Hafsat Tuge

Mijina ya sakeni amma bai bani takardar shika ba cewar Amaryar Tiktok Hafsat Tuge

Idan baku manta ba mun kawo muku labarin yadda wata tsohuwa ta fito ta gayawa duniya cewa, itace Mahaifiyar Hafsat wanda ake kira da Amarya Tiktok ce wanda tace bada bakinsu a matsayinsu na iyayenta suka barta ta shiga harka fim ba.

Bugu da kari abinda yafi tayarwa da mutane hankali shine da aurenta ta gudu ta shiga harkar fim din.

Shine Majiramu ta samu wani labari da take cewa, ita mijinta ya Saketa amma bai bata takarda ba kamar yadda shafin “Hausaloaded” suka wallafa.

Amaryar Tiktok wato Hafsat Tuge tayi bayanin asalin abin da ya faru har ya janyo mata cece-kuce kan tana yin harkar fim da igiyar aure a kanta.

Wanda har yanzu dai ana kaiwa ruwa rana akan jarumar Hafsat Tuge wanda aka ce tana yin fim da auren wani akan ta, inda lamarin a yanzu yake sake daukan hankalun jama’a inda zuwa yanzu gaskiyace take sake fitowa kan lamarin nasu.

Mijin nata dai ya fito ya bayyanawa jama’a cewa shi sam bai saki matarsa ba, inda ma yake ikirqrin cewa da igiyar aurensa a kanta take fitowa tana yin fina-finai, lamarin da ya janyo cikas har ma yayi sanadiyar tsayawar shirin mai dogon zango na zaman aure wato Amaryar TikTok.

Sai dai Hafsat din tayi cikekken bayani akan yadda lamarin nasu ya kasance ita da mijin nata.

Ga bidiyon a kasa domin ku kalla.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button