
Labaran Hausa
Murja Ibrashim ‘yar TikTok ta fashe da kuka tana rokon kada a rushe gidan Rarara kan cin mutuncin da ya yiwa Gwamnan Kano
Murja Ibrashim 'yar TikTok ta fashe da kuka tana rokon kada a rushe gidan Rarara kan cin mutuncin da ya yiwa Gwamnan Kano
Kamar yadda kuka sani dai Mawakiya Siyasa Dauda Kahutu Rarara ya fadawa manyan ‘yan siyasar Kano na jam’iyyar APC magana, wanda hakan ya haddasa cece-kuce.
Dalilin wannan magana da Rarara ya fadawa manyan ‘yan siyasar Kano, a yanzu haka an bayyana cewa, gidan da Mawaki Rarara yake ciki akan hanyar ruwa yake.
Wanda hakan yake nuna cewa, za’a rushe gidan da Mawaki Rarara yake ciki.
Sai dai a yanzu Murja Ibrashim Kunya ‘yar TikTok ta fito tana nuna rashin jin dadin ta akan rushe gidan Rarara da za’a yi.
Inda ta wallafa wata bidiyo a shafinta na TikTok tana bayyana rashin jin dadinta, zaku iya kallon bidiyon dake kasa domin kuga yadda murja take nuna alshininta.
Ga bidiyon a kasa domin ku kalla.