
Na Sayar Da Mota Ta Sannan Kuma Na Sanya Gidana A Kasuwa Don Na Sayar Na Fanso Yayana Daga Gurin Masu Garkuwa
Na Sayar Da Mota Ta Sannan Kuma Na Sanya Gidana A Kasuwa Don Na Sayar Na Fanso Yayana Daga Gurin Masu Garkuwa
Wani mutum mai matsakaitan shekaru ya bayyana cewa ya sa gidajen shi a kasuwa, sannan ya siyar da motar shi sannan ya iya haɗa kuɗin karɓo ‘ya ‘yan shi daga hannun masu garkuwa da mutanen da suka ɗauki ‘ya ‘yan shi guda biyu.
Mutumin mai suna Lukman Aliyu, mai sana’ar kayan ƙarafa, wanda mazaunin garin Ilorin jihar Kwara ne, ya bayyana ma jaridar Punch cewa sai da ya sanya gidajen shi guda biyu a kasuwa, haka nan ya siyar da motar shi da kuma wasu kayayyaki kafin ya iya haɗa kuɗin da zai fanso ‘ya ‘yan shi.
Masu garkuwa da mutane sun ɗauke ‘ya ‘yan na shi Muhiddeen ɗan shekara 15 da kuma Abdulƙadir dan shekara 12 a ranar 13 ga watan Oktoban nan da muke ciki a gidansu dake Aseyori, yankin Alagbado dake ƙaramar hukumar Ilorin ta kudu dake jihar Kwara.
Lukman ya bayyana wa manema labarai cewa, da misalin ƙarfe sha biyu na dare (12am), lokacin suna ƙoƙarin zuwa su kwanta shida matar shi da ‘ya ‘yan shi su biyar, sai matar tashi tace taji alamar kamar wasu sun shigo cikin gidan.
Ya ƙara da cewar yana leƙawa sai ya hangi mutanen suna ta ƙoƙarin yanke ragar sauron ɗakin na sa. Ya ce shida matar tashi sunyi ƙoƙarin suyi ihu domin neman ɗauki daga makwabta amma sai barayin suka fara harbe harbe wanda hakan ya hana kowa fitowa.
“Nayi ƙoƙarin jifar masu garkuwar da kwalabe, amma duk da haka suka cigaba da yin harbi. Daga ƙarshe dai dana fahimci cewa babu makawa sai sun shigo, sai na umarci matata da ta shiga ɗaki ta kulle kanta da ‘yan ‘yan nata, nima na shiga na kulle kaina a banɗaki.
“Daga ƙarshe sunyi nasarar kutsa kai zuwa ɗakin matar tawa inda suka dake ta a ƙirji sannan kuma suka ɗauki yaran mu guda uku. A yayin da suke ƙoƙarin ficewa, wani ɗan sakai ya kai musu harbi inda suma suka mayar masa da harbi, amma harsashin bai yi mishi komai ba.
“A cikin hakan ɗaya daga cikin ɗaya daga cikin ‘ya ‘yan nawa ya samu ya kuɓuta, inda su kuma suka arce da yaran nawa guda biyu.”
Da aka tambaye shi ko sun ɗauki wani abu bayan nan, sai yace eh sun ɗauki wasu ‘yan kuɗaɗen sa sannan kuma sun tafi da jakkar matar tashi da wasu ‘yan kuɗaɗe, haka nan sun tafi da abin sha, da burodi da wayoyi, ciki harda ta wani mutum da ya kawo caji.
Yace da farko da suka kira sun buƙaci a basu naira miliyan ashirin ne, daga bisani kuma suka dawo miliyan goma. Bayan haka sun dawo zuwa miliyan takwas, inda daga ƙarshe aka daidaita a miliyan biyar.
Yace ya siyar da motar shi miliyan ɗaya da rabi, yan uwansa sun haɗa mishi dubu ɗari biyar. Sannan ya siyar da wasu kayayyaki amma duk da haka kuɗin basu haɗu ba. Ya sanya gidajen shi a kasuwa, amma da bai samu mai siye da sauri ba sai yayi amfani da gidajen wajen samun rancen cikon kuɗin da ya bayar aka sako mishi yaran nashi.
Yace da aka gama haɗa kuɗin an bawa wani abokin shi wanda ya kai musu kuɗaɗen. Amma kafin nan sun buƙaci a haɗo musu da kwalebanin giya da kayan shaye-shaye da kuma katin waya. Bayan an kai musu kuɗaɗen sun ƙirga ne suka sako mishi ‘ya’yan nashi
Masu sauraranmu a Koda yaushe bayan Kun karanta wannan labarin zamu so karben a sahen mu na tsokaci.