Advertisement
Labaran Hausa

Na sha wahala babu gida ba mota ba aikin yi gani da yara biyu, cewar wata Bazawara

Na sha wahala babu gida ba mota ba aikin yi gani da yara biyu, cewar wata Bazawara

Wata matashiya ‘yar Najeriya, Edi Mac, ta sanya mutane sun tausaya mata a yanar gizo bayan ta bayyana cikin irin halin da take a rayuwa, kamar yadda shafin “Hausaloaded” suka ruwaito.

Matashiyar wacce take da yara biyu, ta kuma ƙara bayyana cewa bazawarace da yara biyu sannan ita take kula da su ba tare da samun wani tallafi daga wajen tsohon mijinta ba.

Duk da hakan ta tiƙi rawa cikin bidiyon sannan ta bayyana cewa taken rayuwar ta yanzu shine ‘ba wahala.

A kalaman matar ta fara da cewa:

Ina ƙoƙarin nuna cewa komai daidai yake amma a halin da ake ciki nan da mako biyu zan cika shekara 31 a duniya, ba gida, ba mota, ba ƙwaƙƙwaran aiki, bazawara da yara biyu, mahaifin yaran baya tallafawa yaran amma ina cigaba da rayuwata. Taken rayuwata shine ba wahala.

Mutane da dama sun tausayawa matashiyar inda suka kara karfafa mata guiwa, ga kadan daga ciki.

@Vuyani 2 ya rubuta: Nayi gidana da motata ta farko ina da shekara 35 a duniya, sannan daga ƙarshe na samun aikin da nake muradi a ina shekara 36. Lamura na sun sauya cikin watanni shida kacal. Ki yarda da ni ubangiji ba zai bar ki hakanan ba.

@Laytesha ta rubuta: Kakana ya gaya min cewa idan kana da yara, kai mai arziƙi ne.

Emmaculate Mathebula ta rubuta: Yau na cika shekara 30 ban taɓa aure ba, ba aiki, ba mota, ba gida ba yara.

Source of Hausaloaded

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button