
Naje bikin abokina domin na rakashe ashe amryar tasa budurwata ce wacce mukayi shekaru uku tare
Naje bikin abokina domin na rakashe ashe amryar tasa budurwata ce wacce mukayi shekaru uku tare
Wani dan Najeriya ya shawarci maza a kan cewa, kada su kuskura su yarda da mata ko kadan bayan ganin yadda soyayyarsa ta kaya da budurwarsa, kamar yadda “Labarun Hausa” suka ruwaito.
Sambo Mai Hula ta shafinsa na Twitterna @Abdullahiabba, ya bayyana yadda abokinsa yaje bikin amininsa a ranar Lahadi, 16 ga watan Oktoba inda ya gano cin amanarsa da aka yi.
Ga mamakin abokin Sambo, ashe amaryar mai suna Fatima budurwarsa ce wacce suka yi shekaru uku suna soyayya.
A cewar Sambo, abokinsa yayi niyyar auren budurwar amma kwatsam ashe mafarkinsa ba zai tabbata ba.
Kamar yadda ya wallafa: Kada ka kuskura ka yarda da mace domin sai taci amanarka.
Wannan matashin sun kai shekaru uku suna soyayya da Fatima inda yake da burin aurenta kawai sai yaje bikin abokinsa jiya inda ya gano ashe Fatima ce amaryar, kada ka kuskura ka amincewa mace.
Sambo wanda asalin sunansa “Abdullahi Abba Sambo” ya tabbatar wa Legit.ng gaskiyar labarin, inda ya bayyana dalla-dalla yadda lamarin yafaru.
Dan kasuwar ya bayyana yadda lamarin ya auku a karamar hukunmar Ungoggo da ke Jihar Kano.
Rahoto daga👉 Labarun Hausa