Advertisement
Labaran Hausa

Nayi nadamar karuwancin da nayi a baya yanzu na zama abar kwatance da kyamata, cewar Muneerat Abdussalam

Nayi nadamar karuwancin da nayi a baya yanzu na zama abar kwatance da kyamata, cewar Muneerat Abdussalam

Fitacciyar mai maganin mata Muneerat Abdulsalam ta bayyana halin da take ciki na kunci da takaici kasancewar bariki ta yi mata atishawar tsaki, kamar yadda “Labarun Hausa” suka wallafa.

A wata wallafa da tayi yau an ga yadda idonta ya kumbura har tace tana neman makancewa sakamakon mawuyacin yanayin da ta shiga.

A cewarta bata da ko kudin da zata siya wa kanta Paracetamol sabida tsananin talaucin dake damunta, kuma ta tabbatar da shashanci da karuwancin da tayi.

Tace, wannan kadai ya ishi jama’a izina musamman kananun yara masu tasowa su gane cewa, bariki ba abin yibane.

Ga dai cikekkiyar wallatar da tayi a shafinta:

Oh ni Muneerat Abdulsalam haka ratuwata ta koma?, ko kudin sayan paracetamol bani dashi kuma ba mai bani, na zama abin kwatance a idon duniya gani ga wane ya ishi wane tsoron Allah.

Nayi nadamar duk a karuwancin da nayi daga baya da duka shashanci, da barikanci wannan ai shi ake cewa hisabi tun baka mutu ba.

Toh karku kuskura ku sawa yaranku suna munira, kuma ina so ku maidani abin kwatance ga yaranku da jikokai, ina cikin nadamar rayuwar da nayi daga baya, Allah ka yafemin.

Rahoto daga👉 Labarun Hausa

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button