Advertisement
Labaran Hausa

Nayi rashin mai mini babbar addu’a tun lokacin da mahaifiyata ta rasu, cewar jarumi Tijjani Faraga

Nayi rashin mai mini babbar addu'a tun lokacin da mahaifiyata ta rasu, cewar jarumi Tijjani Faraga

Jarumi a masana’antar kannywood “Malam Tijjani Faraga” ya bayyana irin halin kaduwa da ya shiga sabida rashin mahaifiyar sa da ya yi, wato Hajiya Rabi’atu Usman.

Da yake tattauna wa da mujallar Fim kwana uku bayan rasuwar mahaiflyar tasa, MalamTijani ya ce:

Gaskiya ban taba rashin wani dan adam da ya kai mahaifiya ta ba, tun lokacinda ta rasu a rikice nake gaskiya, domin mata ce da duk abin da ya same ni ko na je ne, abu daya take yi tace mani daga hannu a yi addu’a.

Duk abin da ya dame ni ita nake fadawa, kuma idan tayi addu’a cikin hukuncin Allah sai inga saukin abin.

Hajiya Rabi’atu, mai kimanin shekara 89 ta rasu ne a ranar Juma’a 14 ga watan Oktoba 2022, a gidanta dake Unguwar Rogo cikin garin Jos jihar Filato da misalin karfe 12:45 na rana.

An yi mata sallah da misalin karfe 2:05 a babban masallacin garin Jos, Tijjani Faraga shi ne dan ta na hudu.

Haka kuma ita babbar yaya ce ga babban Limamin garin Jos “Sheikh Lawal Adam” wasu daga cikin ‘yan fim da suka je masa ta’aziyya sun hada da.

Abdu Kano “Karkuzu”, Rabi’u Rikadawa, A-Amin Buhari, Usman Mu’azu, Salisu Officer, Murtala Madobi, Abubakar S. Shehu, Sani Ranjeet, TanimuAkawu, Hamza Talle Maifata, Waziri Bado, Oshere, Habun Hajiya, Yusuf Khalid, Maijidda Abbas, Teema Makamashi da Aisha Aliyu.

Allah ya jikan Hajiya Rab’atu da rahama. Ameen Ameen.

Rahoto daga👉 Fim Magazine

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button