Advertisement
Magunguna

Nonon ki jarin ki ‘yar uwa: Hanyar da zaki gyara Nonon ki cikin sauki ba tare da wata illa ba

Nonon ki jarin ki 'yar uwa: Hanyar da zaki gyara Nonon ki cikin sauki ba tare da wata illa ba

Da yawa daga cikin mata basa son kula da jikin su, hakan yana faruwa ne sakamakon sakaci da kuma nuna halin ko in kula dake addabar tunanin su, sannan suna mantawa da irin cikar sura da suke da ita.

Mata tun fil azal an San su da kwalliya, tsafta, da dukkan wani abu makamancin haka wanda yake nuni da tsatso musu kyauwun su a bayyane, domin ta wannan hanyar ne kawai namiji zai gani har ya kyasa kiyi masa a rai.

Wannan wani hadi ne da masana kiwon lafiya su ka samar bayan gudanar da zuzzurfan bincike. Kuma babban abin farin ciki game da wanan hadi, baya ga saukin hadawar sa, an jarraba an ga fa’idarsa, sannan ba shi da wata illa ga lafiyarmu, saboda dukkan kayan hadin dangogin abincin da mu ke ci yau da kullum ne.

Kamar dai yadda kowanne magani yake, ana bukatar kayayyakin da za’a samar da shi, haka ma wannan yana da nasa mahadin. Abubuwan Da Ake Bukata sune kamar haka:

– Gyada
– Hulba
– Ridi
– Alkama
– Shinkafa

Wadannan kayan abinci ake bukata mace ta tanada. Abin da zata yi shine, ta samu garinsu. Abin nufi kamar shinkafa, sai ta gyara ta sosai ta daka ko nika yadda za ta samu garinta. Haka za ta yi wa gyada, ridi, da alkama. Ita kuwa hulba sai ta sayo garinta, shi kuma karas sai ta shanya shi ya bushe sannan ta samu garinsa.

Bayan ta sami garin wadannan abubuwa da mu ka ambata a sama, sai ta hada su waje guda ta gauraye, daga nan ta adana su a mazubi mai tsafta, kuma mai murfi.

Yadda za ta yi amfani da wannan hadin gyaran nono shine, za ta sami madara ‘Peak’ idan son samu ne, ta ke zuba wa ta sha a kullum. Za ta sha mamaki matukar ta juri amfani da wannan hadin gyaran nono, domin kuwa nononta zai dawo tamkar na budurwa, da iznin Allah.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button