Advertisement
Labaran Hausa

Ra’ayoyin Malaman Addinin Musulunchi Kan Hukunchi Kisa Ta Hanyar Rataya r Da Aka Yanke Abduljabar Kabara

Ra'ayoyin Malaman Addinin Musulunchi Kan Hukunchi Kisa Ta Hanyar Rataya r Da Aka Yanke Abduljabar Kabara

Kano A ranar Alhamis, 15 ga watan Disamba 2022, kotun shari’a ta yanke hukuncin kisa ga malamin addinin nan, Sheikh Abduljabbar Nasiru Kabara.

A wannan rahoto, Legit.ng Hausa ta tattaro abin da wasu daga cikin malaman musulunci suke fada kan hukunci da lbrahim Sarki Yola ya zartar.

Dr. Ibrahim Disina, shahararren malamin addinin Musulunci a garin Bauchi, yana cikin wadanda suka fara yada labarin, amma bai ce komai ba a kai.

Shi Dr. Kabir Asgar a rubutun da ya yi a Facebook, ya yi godiya ga gwamnatin Kano, kotun shari’a, malaman addini, da daukacin al’ummar musulmai.

Malamin yake cewa Alkalin da ya yanke hukunci ya farantawa al’umma rai. A karshe ya ce Allah (SWT) ya sa a samu karfin gwiwar zartar da kisan.

Muhammad Rabi’u Rijiyar Lemo ya yi tsokaci a kan shari’ar, ya ce tun farko Abduljabbar Nasiru Kabara ya yi kalaman batanci a kan Manzon Allah.

A cewar Dr. Muhammad Rabi’u Rijiyar Lemo, malamin ya gagara nuna inda lafazin ya zo a littafan musulunci, a karshe yake cewa gaskiya ce tayi halinta.

“Mutum ne ya yi kalaman Batanci ga Manzon Allah S.A.W kuma ya ce, wadannan kalaman suna cikin littattafan malaman Musulunci, ya ma ayyana sunayen wadannan littattafai, tare da juzui da shaf. Aka nemi ya buda wadannan littattafai ya nuna inda wadannan kalamai suke amma ya gaza, sai ya koma kame-kame da cewa ai shi da ma’ana yake riwaya. Ita ma ma’anar aka ce nuna lafazin da ya zo da wannan ma’anar shi ma hakan ya gagara.

Alhamdu tillahi, yau gaskiya ta kara bayyana.”Muhammad Rabi’u Rijiyar Lemo

Farfesa Mansur lbrahim Sokoto, malamin hadisi a Sokoto, ya ce jiya rana ce ta farin ciki ga muminai saboda an kare kimar Annabi SAW da sahabansa.

Rana ce da muminai suke murna da taimakon Allah. Allah mun gode maka. Ka kara kare martabar manzonka da iyalansa da almajiransa da masoyansa har ranar tashin alkiyama. Ka tozarta, tare da wulakanta duk mai keta alfarmarsu.

Alhamdu lillah

– Farfesa Mansur lbrahim Sokoto

Farfesa Mansur Ibrahim Sokoto

Shi kuwa Farfesa lbrahim Maqari ya sha bam- bam, yana ganin banbamcin siyasa ya jawo aka zartar da wannan hukunci a kan Sheikh Kabara ba komai ba.

lbrahim Maqari ya ce a tarihi, mafi yawan wadanda aka kashe da sunan zindikancin, ba shi ne asalin laifinsu ba, illa iyaka ana fakewa da wannan ne kurum.

“Mafi yawan wadanda aka kashe saboda tuhumar zindikanci a tarihi idan mai karatu ya zurfafa bincike zai samu rikicin siyasa ne ya hadasu da masu mulki.. Amma ba zindikancin ne dalilin kisan ba.”

Farfesa Ibrahim Maqari

Muhammad Sani Umar Rjiyar Lemo ya jawo wata aya daga Suratul Hijr a shafinsa na Facebook.

Wannan aya ta Al-Kurani tana nuna Allah madaukakin Sarki (SWT) zai kare Annabi Muhammad (SAW) daga izgilancin duk wasu masu yi masa izigili.

Kamar yadda shafin Hausalegit Nigeria Suka Wallafa

Masu sauraranmu a Koda yaushe bayan Kun karanta wannan Bayanin zamu so karben ra’ayoyinku a sahen mu na tsokaci.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button