Advertisement
Labaran Hausa

Rahama Sadau tayi martani akan matashin da yace zai iya sayar da gonar gadon su a kanta

Rahama Sadau tayi martani akan matashin da yace zai iya sayar da gonar gadon su a kanta

Wani matashi mai suna lbrahim Abdullahi sulaiman shugaba yayi fostin a shafinsa na sada zumunta facebook inda ya wallafa cewa, a kanki zan iya sayar da gonar gadon mu kwaran kwatsa, Rahama Sadau.

Shidai so babu ruwansa yana iya fadawa kan kowa shi wannan matashin tsananin son da yake yiwa jaruma Rahama sadau har ya kai ga cewa, zai iya asarar gonar gadon su domin ita.

Wannan rubutun da matashin ya yi ya dauki hankulan mutane sosai inda nan take jarumar tazo tayi masa martani, wanda nasan kowa yana son yasan mi jarumar tace masa.

Jarumar a karkashen comments section tayi masa martani kamar haka, amma kafin jarumar tayi masa martani sai da tayi masa dariya inda ta sanya emoji mai alamar dariya sa’anan tace masa.

Ka bar mana muyi noma tare, nan take Ibrahim yace, Rahama Sadau wayyo Allah na ranki ya dade ai sai abin da kika ce yasin.

Shafin “Hausaloaded” sun tattaro muku martanin da wasu suka yi a karkashin fustin din wannan matashi, ga kadan daga ciki.

Nasbil zaman mkrc: Rahama Sadau yana masifar sonki dan Allah ki amsa masa ko sau 1 kina sonshi.

Gambo usman : Ina rokon Allah ubangiji ya sauwake maka wannan cutar da take damunka.

Gimbiya halima : Aramma en mu lbrahim Abdullahi Sulaiman Shugaba iska na wahalar da me kayan kara, zo na rakaka Dawanau me Npip ya rage mana Hanya.

Rahoto daga👉 Hausaloaded

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button