
Raryuwar Da Muneerat Abdulsalam Ta Shiga Yanzu Ta Ishi Su Safara’u Da Rahama Sadau Darasi
Raryuwar Da Muneerat Abdulsalam Ta Shiga Yanzu Ta Ishi Su Safara'u Da Rahama Sadau Darasi
Kamar yadda kuka sani a satin da ya gabata ne ake ta magana kan dana sanin da muneerat tayi kan maganganu da bazu dace a kafar sadarwa wadda yanzu haka aka Bayyana Cewar tana fama da rashin lafiya
Inda a yau kuma shafin garkuwan arewa dake kan manhajar Instagram Yanzu Cewar
garkuwanarewa_ RAYUWAR MUNEERAT ABDULSALAM: Darasi Ga Safara’u Da Rahma Sadau
Da Ire-irensu
Daga Imam Indabawa Aliyu
Na ga rubutun wata shahararriyar mata mai suna Muneerat Abdulsalam wacce ta ce ta yi matukar nadamar munanan ayyukanta da ta yi a rayuwarta, a halin da take ciki ta ce ba ta da ko kudin siyan paracetamol wanda hakan ya sa take rokon al’umma da su taimaka mata.
Muneerat dai ta yi kaurin suna wajen bidiyon batsa da yada hotunanta masu dauke da shigar banza sai dai zuwa yanzu tuni duniya ta yi mata atishawar tsaki domin ta
Allah wadai da karuwancin da ta dinga yi a rayuwarta tana mai cewa rayuwarta kadai ta isa ta zama darasi ga masu hali irin nata.
Wannan ya isa darasi ga irinsu Safara’u da suka kulla abota da shaidan suka tare a bariki da wani dan iskan yaro mai suna 442 suna iskanci da fitsara iri-iri.
Hakika duniya abar tsoro ce, duk abin da mutum ya shuka sai ya girba.
Haka yarinyar nan mai suna Rahama Sadau babu irin fitsarar da ba ta yi tana shigar banza ta dora hotunan a media, idan aka yi mata nasiha har izgili take wai ai gonarta ce, a bar ta ta girbi abin da ta shuka.
Saboda fitsara na yarinyar nan har fitowa ta yi ta ce wai ita ba cikakkiyar budurwa ba ce ta riga da ta rasa budurcinta tuntuni kuma ba ta hanyar aure ba.
Wani labarin ma da na gani wai an ce ta ce ba ta san adadin cikin da ta zubar a jikinta ba kuma har alfahari take ko a jikinta.
Ga wata nan ma mai suna Nafisat Abdullahi da sauransu suna amfani da yaren Hausa suna koyar da shigar banza, To lallai Allah abun tsoro ne idan ya tashi kama mutum ba zai ji dadi ba, don haka gwara mutum ya yi amfani da damarsa ya tuba ya koma aikata ayyuka masu kyau.
Sauran ‘yan matan fim masu shigar banza suna lalata tarbiyya wadanda suka fake da fm suna karuwanci mai lasisi suna rike manyan wayoyi da hawa manyan motoci, kuma suna zuwa kasashen duniya yawon shakatawa duka wannan ya zama darasi a gare su.
Karuwanci ba abu ne mai kyau ba, kuma mai aikata shi ba zai sami yadda yake so ba.
Masu sauraranmu a Koda yaushe bayan Kun karanta wannan labarin zamu so karben a sahen mu na tsokaci.