Advertisement
Labaran Hausa

Rashin kudin makaranta ne yasa na fara harkar fim a kannywood, cewar jarumi Adam A Zango

Rashin kudin makaranta ne yasa na fara harkar fim a kannywood, cewar jarumi Adam A Zango

Gidan Radio freedom dake jihar kano sunyi wata zantawa da jarumi Adam A Zango inda yabayyana cewa, dalilin fara harkar fim a rayuwarsa sabida rashin kudi shi yasa ya koma Masana’antar kannywood, kamar yadda “Hausaloaded” suka wallafa.

Adam A Zango ya bayyana hakan a tattaunawar sa da Freedom Radio inda yake cewa, gazawar rashin kudin cigaba da karatun ne yasa shi fara sana’ar hakar ma’adanai, sai dai daya gano bata karbeshi ba ya koma harkar film.

Zango yace, shi mutum ne mai son neman na kansa, kuma ya shigo masana’antar kannywood ashekara ta 2003.

Rahoto daga👉 Hausaloaded

A wani labarin kuma

Fitacciyar jarumar fim Rahama Sadau ta caccaki masana’antar Kannywood da Hukumar tace fina-finai kan yanda aka dakatar da jaruma Safiya Yusuf, wacce aka fin sani da Safara’u bayan bayyanar bidiyonta.

An dakatar da Safara’u daga masana’antar fina-finan Hausa a shekarar 2022 bayan bayyanar bidiyonta.

Zakakurar jarumar tace kawayenta ne suka fitarda wannan bidiyonta wanda hakan ya durkusarda sana’arta a wannan lokacin.

Safara’u ta fara shuhura ne a fim mai dogon zango wanda gidan talabijin din Arewa 24 suke haskawa mai suna Kwana Casa’in, tace tayi zaman gida na tsawon watanni uku domin gujewa zagin jama’a.

Jarumar ta kara da cewa, sai data kusa goge dukkan asusunta na soshiyal midiya sabida zagin da take sha daga jama’a.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button