Advertisement
Labaran Hausa

Rayuwar zaurawa gaba dayan ta abar tausayi ce ya kamata ana taimaka musu, cewar jamila Ibrashim

Rayuwar zaurawa gaba dayan ta abar tausayi ce ya kamata ana taimaka musu, cewar jamila Ibrashim

Wata fitacciyar mata da ta shahara a Facebook mai suna “Jamila Ibrahim” tayi fashin baki dangane da halin da zawarawa ke shiga bayan mutuwar auren su.

Tayi bayani ne a matsayinta na bazawara tare da hasko irin kalubalen da take fuskanta tare da irin kallon da al’umma ke yi musu, a wata wallafa da tayi a shafinta na Facebook a ranar 5 ga watan Oktoba, kamar yadda “Labarun Hausa” suka ruwaito

Kamar yadda ta bayyana, akwai mutane masu gutsiri tsoma a kan zawarawa amma ana rasa wadanda ke tallafa musu da kudi komai kankantarsu.

Ta fara da cewa: Wato rayuwar zawarawa gaba daya abin tausayi ne idan kuka rabu da miji ko kuma mijin ki ya rasu, idan iyayenka ba masu kudi ba ne daga ranar kai zaka yi kanka komai na rayuwa.

Idan baka da sana’a ko aikin yi sai mai imani ne zai iya kama kansa, shi yasa za kaga wasu zawarawa na yawon gari wurin bin maza.

Da iyaye da ‘yan uwa zasu taimaka da jari da abin zai zo da sauki, ta bayyana yadda wahala ke karuwa idan mata sun rabu da mazajen su yayin da suke da yara kuma aka sakar musu dawainiyar yaran.

Ta bukaci masu halin taimako da su dinga tallafawa mata idan sun ga sunzo kan yanar gizo suna nema, kowa tasan abinda take ji.

A cewar ta, kada mutane su ganta fara kuma da kibarta bata da kudi,  sannan akwai mazan da ba sa auren mace da zarar sun gane tana da yara.

Daga karshe ta roki jama’a da cewa, idan ba zasu yi musu addu’a ba kada su kashe su don babu macen da zata rabu da miji idan har yana bata kulawa.

Rahoto daga👉 Labarun Hausa

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button