Advertisement
Labaran Hausa

Sanadiyar tiktok na fara sayar da maganin mata, cewar Ashiru mai ushirya

Sanadiyar tiktok na fara sayar da maganin mata, cewar Ashiru mai ushirya

Gidan rediyo Dala FM dake jihar kano sun samu zantawa da Ashir Idris wanda aka fi sani aidress a Tiktok, ko kuma mai Wushirya domin fattatakar matan TikTok dake shigar da bata dace ba.

Tauraron TikTok Ashir Idris da aka fi sani da Mai Wushirya yace, sakamakon TikTok ya shiga sayar da magungunan mata.

A zantawarsa da tashar Dala FM dake Kano Ashiru Idris yace, ya soma ne da yiwa wasu talla kafin daga bisani ya rikide.

Idris yace, ya sami riba mai yawa a sanadin TikTok, inda ya kara da cewa baya damuwa da wadanda ke zaginsa ko kiransa da dan daudu, domin hakan alamun nasara ne a wajensa.

Da yake martani kan hadewar Murja Ibrahim Kunya da mawaki Mr 442 mai Wushirya yace, tafiyarsu da ita ba zata yi karko ba, Yayin tattaunawar dai Ashir Idris ya bada tarihin rayuwarsa da kuma dalilin shigarsa TikTok.

Zaku iya kallon bidiyon dake kasa domin kuji cikekkiyqr tattaunawar da aka yi da shi.

Ga bidiyon a kasa domin ku kalla.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button