
Shahararran mawakin kasar Pakistan ya bar kida da waka zai mayar da hankalinsa kan addinin Musulinci
Shahararran mawakin kasar Pakistan ya bar kida da waka zai mayar da hankalinsa kan addinin Musulinci
Wani mawaki dan kasar Pakistan ya yanke shawarar yin bankwana da wake-wake domin mayar da hankali kan addinin musulunci.
Mawakin mai suna “Abdullahi Qureshi” ya bayyana hakan a shafukan sa na sada zumunta.
Abdullahi Qureshi sanannen mawaki ne wanda mutane da dama suka san da shi ta hanyar wakokin sa a YouTube, kamar yadda “Labarun Hausa” suka wallafa.
Mawakin wanda yayi wata waka mai suna “Awaz Do” ya sanar da wannan hukuncin da ya yanke ne dai a shafinsa na Facebook.
A kalamansa: Alhamdulillah na gamsu matuka da wannan hukuncin da na yanke, sannan ina matukar son ganin na gano hakikanin gaskiya.
Addu’a ta itace Allah ya taimake ni a wannan sabuwar rayuwar dana fara, a cewar sa ba zai kara fitowa a cikin tallace-tallace ba ko yin wasa a wurin shagalgula ba.
Don Allah kada ku tuntube ni kan irin
wadannan abubuwan, a yayin da ya nuna matukar godiyar sa bisa goyon baya da kaunar da aka nuna masa, ya kammala jawabin sa da cewa:
Idan ana bukata ta domin fitowa ko yin wani kamfen a kafafen sada zumunta, wanda kuma nake da ra’ayi sannan basu kaucewa koyarwar addinin mu na musulunci ba, zan yi farin cikin bada gudunmawa ta.
A ranar 6 ga watan Oktoban 2022 ne “Abdullahi Qureshi” ya sanar da wannan hukuncin nasa na barin wake-wake bisa dalilan sa da suka shafi addini.
Ya samu goyon baya sosai a kafafen sada zumunta bisa wannan hukuncin da ya yanke.
Yayi karatun sa kwalejin Bahria a Islamabad, inda aka haife shi kuma ya taso.
Ya samu digirin sa na farko a jami’ar National University of Sciences and Technology, a fannin aikin jarida.
Abdullahi Qureshi ya fara yin kade-kade cikin tawagar makada a Islamabad kafin ya fara yin wakoki.
Rahoto daga👉 Labarun Hausa