Advertisement
Labaran Hausa

Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa Yaje A ‘Late Comer’ Sai Yi Wuff Da Gwarzuwar Muzabaqar Alqur’ani Ta National

Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa Yaje A 'Late Comer' Sai Yi Wuff Da Gwarzuwar Muzabaqar Alqur'ani Ta National

Sheikh Daurawa, fitaccen malamin addinin islama a Najeriya ya yi nasarar yin wuff da zukekiyar budurwa a matsayinsa na Late Comer.

Kamar yadda bayanai su ka nuna, duk da tarin samari na jami’a da wandanda su ka nemi aurenta a hadda kasancewarta mahaddaciya amma malamin ne ya kasance zakara.

An samu rahotan ne a ajin Northern Habiscus inda wata daga ciki ko wani daga ciki ya shaida wa malamar aji ita kuma ta yada har muka samu bayanin.

Sunan budurwar Haulat kuma ta lashe masabakar kasa wacce ake zargin daga nan ne ma malamin ya ganta har yayi sha’awar aurenta.

Nan da nan mutane su ka zabura su na mamakin yadda malamin ya samu nasarar samun damar wannan kyakkyawar budurwa.

Ana sa ran za ayi auren ne a ranar Asabar mai zuwa. Allah ya nuna mana kuma ya sanya alkhairi. Ameen summa Ameen.

Masu sauraranmu a Koda yaushe bayan Kun karanta wannan labarin zamu so karben a sahen mu na tsokaci.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button