Labaran Hausa

Sheikh Bello Yabo yayi zazzafan martani ga shugaba Buhari kan canja kudin Nageriya

Sheikh Bello Yabo yayi zazzafan martani ga shugaba Buhari kan canja kudin Nageriya

A yan kwana kin nan da ake ta cece-kuce akan chanza kudin Nigeria da za’a yi wanda kowa yana tofa albarkacin bakinsa, wanda kowa yana hasashen cewa tabbas za’a yi hasara sosai.

Wasu na cewa, wannan chanza kudin zai kawo durkushewar tattalin arzikin Arewacin Nigeriya sabida yawancin ‘yan Arewa mazauna kauye zasuyi hasara sosai da sosai.

Wasu na cewa, a’a ai wasu manya manyan ‘yan kasuwa da ‘yan siyasa ne suka tara kudi a gida jibge wanda idan aka yi wannan canja kudi zasuyi hasara.

Ash sheikh Bello Aliyu Yabo Sokoto yayi tsokaci sosai akan wannan canja kudi da za’a yi, inda yakawo tarihin yadda ya canja kudin Nigeria a lokacin da ya karbi mulki soja mallam yayi bayyani dala dala.

Kamar yadda shafin “Hausaloaded” suka tattaro bayanin Malamin yana cewa:

Wai chanjin kudi ! Kun tabbatar da tuwo bai canja sunai 1984 haka yayi fa kurma yaga abinda ya faru ga Nigeria ga ba daya da mutanen Nigeria da tattalin arzikin Nigeria l, shine chanjin kudin nan sanadiyar karewar tattalin arzikin Nigeria.

Yara kuke kuje ku samu dattijai irin mu ku tambayesu kafin Buhari idan mutum zaije haji, alhazzai mu na Nijeriya idan zasu tafi haji babu ruwansu da canja kudi ka sanya ko nawa gareka ka tafi dasu Makkah, ana amsa duk inda kaje ana amsa kudin Nijeriya sai yazo ya canja kudi cikin dan lokaci kankani.

Shikenan bakin date line yana cika duk wani mai bakin magana ina tuna har margayi mai martaba sarkin musuimi Abubakar na ukku yayi magana yace, dan Allah a kara lokaci yace ko minti guda ba’a karawa kuma ko bana haka za’a yi.

Naji wasu malamai suna ta kiraye kiraye suna ta rokonsa nace kun bata lokaci bakusan mutumin ba shiyasa wai ka ayi aean wuce wurin tunda har an bugo kudin ko baku gani hotunsu ba.

An kashe biliyoyin kudi kuma kace ka ayi in ba’a yi ba ya za’a yi da kudin da anka bugo ai magana ka’ayi ba ta taso ba hmm.

Sa’a nan duk lokacin da anka sa kuma bai kara ko kwana gudu haka ankayi ko wan canlokaci 1984 mutane sun kayi ta hasara, bakin lokacin duk wanda bai canja ba to wannan kudin basu da banbanci da sansanmin leaf.

Mutane da nan gida da waje sunkayi hasara mai yawa tun lokacin nan kasashe sunka daina karba kudin Nijeriya.

Sa’a nan mutane da yawa anka jawa asara, naji wani malami lawal Abubakar Shuaibu Kano yana bayyani cewa wasu mutane ne yake targeting suna nan sun tara kudi dan haka bari ayi canjin kudi suyi asara malam lawal yace, wadannan da kake targeting ko anyi canjin kudi ba sune zasuyi asara ba wadanda baka zato talakawa bayin Allah sune zasuyi asara.

Wadanda sunka wahala sunka samu kudi wadanda sunka haka donka kai sune zasuyi asara, mafi yawan wadannan da kake targeting duk mafi yawan masu aikin banki yaran sune.

Malam ya kara da cewa, sa’a nan yanzu misali ina da naira billiyan biyar sai inkira manajan banki manaja eh dan Allah ga kudina nan kun fara canji eh ga billiyan biyar dina nan a canja min okay.

To ya za’a yi zan baka naira miliyan dari ukku kai da yaranka shin kana ganin shekara nawa zai yi kafin ya samu wannan kudin?, bai canjamin in kaje da naira dubu dari zai dube ka to saboda haka basu zasu asara ba.

Talakawa nan sune zasuyi asara masu noman tanka, noman rani da sauransu sune zasuyi asara haka za’a yi tayi kuje banki tunda safe har maraice ace ku dawo gobe har date line ya cika shikenan anka barsu da buhu huwa sun zama shara shi a sanadiyar karewar mutane.

Sa’a nan yaji iri bacin zagi da anka yi mai
lokacin kuma yasan irin yadda tattalin arzikin Nigeria da ‘yan Nijeriya sunka shiga, amma dan kusan tuwo ba’a canja mai Suna.

Rahoto daga👉 Hausaloaded

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button