Advertisement
Labaran Hausa
Trending

Sheikh Gumi Ya Caccaki Gwamnati Kan Chanza Takardun Kudi Sannan Kuma Ya Bayyana Matsolalin Da Hakan Zai Haifar

Sheikh Gumi Ya Caccaki Gwamnati Kan Chanza Takardun Kudi Sannan Kuma Ya Bayyana Matsolalin Da Hakan Zai Haifar

Sheikh Ahmad Gumi ya caccaki kokarin babban bankin Najeriya na sauya wasu takardun Naira inda ya kwatanta lamarin da halaka kai ta fannin tattalin arzikin yan Najeriya balle mazauna kauye.

Daily Trust ta rahoto cewa, kamar yadda yace, kashi 80 na yan Najeriya mazauna kauye ne kuma sun dogara da tsabar kudi domin siye da siyarwa.

Gumi yace duk wani tsari da zai mitsike zagayawar kudi tsabarsu zai zama tamkar ibtilai ga kasar.

Ya kara da yin bayanin cewa tsarin ba zai taba hana masu garkuwa da mutane kudi tsabarsu ba saboda zasu iya yanke hukuncin karbar kudin fansa a dala da sauran kudaden ketare kuma hakan ya matsantawa rayuwar jama’a.

“Mutanen dake siyar da kayayyaki zasu fada maka cewa da yawan yan Najeriya basu da kudi, don haka yan kasuwa suna ta taíka asara.

A wannan wurin duk abinda zai kawo tsaiko ga yawon kudi zai zamo ibtilai a kasar i nan.

“Da yawan hukunci masu kyau ana aiwatar dasu ne a lokacin da bai dace ba. Akwai yuwuwar wannan zai kasance wani.

Duk dai yadda wadanda suka kawo tsarin zasu kuranta shi, amfanin dai ba kamar yadda ake tsammani bane tunda halin da ake ciki na bayyana rashin dacewa Daga bisani.

“Kashi 80 na yan Najeriya musamman yan kauye suna amfani da tsabar kudi ne.

Fannin kwatsam na komawa amfani da kudin da ba tsaba ba yana nufin karuwar talauci a cikin kankanin lokaci.

“Wannan shirin ba na gwamnati bane dake iya bakin rai.

Idan da akwai amfanin irin hakan, yana zuwa ne bayan shekaru masu yawa na matsanancin talauci da matsin rayuwa wanda babu gwamnati mai fatan alheri da ya dace ta mika mulki a hakan.

Da a ce an fara tun 2015, hakan na iya zama daidai tunda gwamnatin ce zata dandana kudarta kan hakan.

Mu shaida ne kan hana achaba, siyar da fetur da datse sadarwa a jihohin da yan bindiga suke cin karensu babu babbaka.

Hakan bai shawo kan komai ba sai dai azabtar da jama a.

“Wannan na nuna cewa gwamnati bata duba komai na hukuncinta masu matsala.”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button