Advertisement
Labaran Hausa

Shin a mawakan Kannywood Ado Gwanja ne bayan taimakawa ‘yan uwan sa

Shin a mawakan Kannywood Ado Gwanja ne bayan taimakawa 'yan uwan sa

Tun bayan labarin kyautar N50,000 da Dauda Kahutu Rarara ya bai wa Sa’idu Isa Gwanja a watan azumin da ya gabata, wanda shi Gwanja ya mayar tare da martanin ba yaso sabida an shiga kafafen yada labarai an yayata shi, jama’a sun yi ta sharhi kan lamarin.

Wasu suna ganin abin an yi shi ne da wata manufa don a nunawa duniya cewa, duk da shaharar da Ado Gwanja ya yi a fagen waka, amma sai da ya bari aka yi wa dan’uwan sa kyauta ta cin mutunci.

Masu wannan maganar suna ganin cewa, karan Ado Gwanja ya kai tsaikon da ya kamata a gani a jikin na kusa da shi ko kuma ‘yan uwa da dangin sa kamar yadda ake ganin arzikin wakar sauran mawakan dake tashe a yanzu, irin su Naziru Sarkin Waka, Rarara, Ali Jita da Aminu Ala a jikin na kusa da su da ma dangin su.

Kamar Ali Jita, duk wasu abubuwa nasa za kaga kannen da yayyen sa ne a kai, kuma an sha ji yana yi masu kyautar gidaje da motoci, hakama Naziru da ‘yan uwan sa.

Duk da yake wasu na ganin kyautar Rarara cike take da siyasa, amma dai na kusa da shi su na amfana.

Ko Tijjani Gandu da ake ganin bai shiga cikin manyan mawaka ba sosai, ana ganin na kusa da shi a tare da su, to amma me ya sa Ado Gwanja ya fita da ban Domin idan ka dauki yayan sa, Saidu Gwanja, ai an nuna duniya ya na bukatar taimako daga Ado, musamman a yanzu ma da ko motar hawa ba shi da ita, bayan ga tsala-tsalan motoci Adon ya na hawa.

Lallai ya kamata ace ko bai ba shi a cikin suba, to ya saya masa ta kasa da su don shi ma ya samu ya yi “warr”, a daina ganin sa yana yawo a kasa ko cikin a dai-daita Sahu.

Ganin yadda surutan suka yi yawa kuma sun ki karewa, mujallar Fim ta nemi jin ta bakin Ado Gwanja din amma duk lokacin da muka kira wayar sa ba ya dagawa, kuma mun je ofishin sa dake Titin Gidan Zu a Kano har sau biyu ba musamu ganin sa ba.

Amma dai mun sami zantawa da yayan nasa “Saidu lsa Gwanja” wanda a kan sa maganar ta taso, inda ya ce:

To ka san shi abu na rayuwa kowa da yadda yake kallon sa, kamar yadda ake ganin sauran mawaka suna yi wa ‘yan uwa da dangin su hidima, to mu ma dai ba zamu ce ko kadan ba a yi mana ba, don ana yi mana dan abin da ya sauwaka.

Kuma ka san kowa da yadda nasa tsarin yake, don haka ko da an ga bai yi ba ta yiwu nasa tsarin kenan.

Da muka tambaye shi ko gaskiya ne a yanzu bashi da motar hawa sai ya ce:

To idan ka lura tsawon lokaci motoci kala nawa na yi?, don a yanzu ba ni da mota ko abin zai dame ni zan dauka cewa yanayi ne na rayuwa, amma dai idan zan samu a yanzu ina so.

Rahoto daga👉 Fim Magazine

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button