
Shin wacce kalar mazakuta kake da ita wacce ta karkarce ko wacce ta mike domin kasan a matsayin da kake
Shin wacce kalar mazakuta kake da ita wacce ta karkarce ko wacce ta mike domin kasan a matsayin da kake
SHIN AZZAKARIN KA WANE KALA NE A CIKIN WADAN NAN SANNAN DAIDAI YAKE KO AKASIN HAKA??.
Health line ta rawaito cewa akwai akalla kalolin Azzakari guda 20,wanda kuma kowanne a ciki daidai yake bashi da matsala.
Kuma suka ce kowanne a ciki zaka iya gamsar da iyalin ka dashi,muddin kasan yadda ake kwanciyar aure dashi (kwanciyar jima’i).
Amma a wannan bayanin zamu kawo kadan daga cikin rabe rabin su saboda yan uwa suji dadin karantawa cikin sauki.
KA WASU DAGA CIKIN KALOLIN AZZAKARIN(PINEL TYPE).
1. Azzakari wanda ya kalli sama(Curve upward)ma’ana wanda yankan kaciyar sa idan ya mike yake kallon sama.
2. Azzakari wanda ya kalli kasa(Curve downward) ma’ana Azzakari wanda idan ya miki sai kaciyar da kalli kasa.
3. Azzakari wanda ya karkace ya kalli hagu(C-Shape) ma’ana wanda Azzakarin sa idan ya miki sai ya kalli dama,ko kuma ya kalli hagu.
4. Azzakari wanda yake a miki chak(Straight)wannan Azzakarin idan ya mike yana tsayawa ne kamar sanda,shi baiyi sama ko kasa ba kuma bai karkace ba.
5. Azzakarin da farkon sa babba ne amma karshen sa dan karami(Bigger base-with Narrow head)shi wannan Azzakarin daga farkon sa zaku ganshi da kauri da girma, amma idan ka kalli wajen yankan kaciya sai ka ganshi babu kauri.
6. Azzakarin da idan ya mike zaka ga farkon sa karami amma daga karshen sa wajen kaciya zaka ganshi babba(Narrow base with larger head.
Akarshe.
Akwai wata cuta da ake kira Peyronie’s disease wannan cuta tana sa Azzakarin mutum ya lankwashe, amma yadda zaka gane idan cutar ce shine,gaban ka lokacin daya mike zai rika yi maka zafi ciwo sosai.
Musamman ta bangaren daya lankwashe, kuma da wahala wanda yake fama da wannan matsala ya iya saduwa da mace domin ciwo da zafin da zai rika ji a gaban nasa.
Haka na gaban baya iya shiga farjin mace saboda yadda ya lankwashe ya karkace sanoda haka harka daga hankali don kaga gaban ya yayi lankwasa indai baya maka zafi ko ciwo wannan ba abin damuwa bane.
KARIN HASKE.
A takaice wadan nan sune kalolin da zamu iya bayani a wannan sakon namu nayau insha Allah a bayani na gaba za muyi bayani akan yadda tsawo da girma Azzakari ya kamata ya kasance na daidai ko kankancewa.
Allah yasa mudace.