Labaran Hausa

Subhanillahi Yadda Budurwa Ta Kashe Saurayinta Da Wuka A Nasarawa

Subhanillahi Yadda Budurwa Ta Kashe Saurayinta Da Wuka A Nasarawa

Rundunar ƴan sanda ta tabbatar da cafke wata mata a Unguwar Gwari da ke Ƙaramar Hukumar Karu a jihar Nasarawa bisa zargin kashe saurayinta da wuka.

Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, PPRO, DSP Ramhan Nansel, ya fitar a jiya Juma’a, a Lafia, babban birnin jihar Nasarawa.

“Rundunar ƴan sandan da ke aiki da sashin Mararaba ‘A’ karkashin jagorancin CSP Musa Babayola sun cafke wacce a ke zargin bayan an kai rahoton faruwar lamarin ga ƴan sanda.

“Bincike na farko ya nuna cewa lamarin ya faru ne a bayan Otel din City Rock, Mararaba da misalin karfe 3:30 na safe ranar Juma’a.

“An kama wacce ake zargin kuma an gano wukar da aka yi amfani da ita wajen aikata laifin bisa ga umarnin kwamishinan ‘yan sanda, Adesina Soyemi,” in ji PPRO ɗin.

Kakakin ya kara da cewa an mika wanda ake zargin zuwa sashin binciken manyan laifuka na jihar a Lafia domin ci gaba da bincike tare da gurfanar da wacce ake zargin a gaban kuliya.

Masu sauraranmu a Koda yaushe bayan Kun karanta wannan labarin zamu so karben a sahen mu na tsokaci.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button