Advertisement
Labaran Hausa
Trending

Subhanillahi Yadda Dan Aikin Ban Ruwa Fulawa Gida Ya Dirgawa Yaran Mai Gidansa Uku Ciki Duk Da Iyayensu Daya

Subhanillahi Yadda Dan Aikin Ban Ruwa Fulawa Gida Ya Dirgawa Yaran Mai Gidansa Uku Ciki Duk Da Iyayensu Daya

Wani rahoto ya bayyana yadda mai ba wa fulawa ruwa a gidan wani attajiri da ke Kenya ya dirka wa ‘yan mata uku ‘yan gida daya ciki

Tsohon dan majalisa, Shehu Sani ya wallafa wannan labari a shafinsa na Facebook

A cewarsa, duk da yadda iyayen ‘yan matan uku ke da tsanani inda su ke yawan rufe su a gida ba tare da barinsu su yi tarayya da kawaye ba, sai ga shi mai ba fulawa ruwa a gidan ya yi musu ciki.

An samu bayanai akan cewa mutumin ne kadai wanda ake bari yana shiga gidan har yake iya harka da su.

Sai dai ashe akwai wata harkalla da ke shiga tsakaninsa da ‘yan matan inda yake lalata da duk ukun ba tare da sanin iyayensu masu tsananin addini ba.

Bayan samun labarin hakan, iyayensu sun yi matukar mamaki akan yadda hakan ya faru duk da yadda suke iyakar kokarin su akan yaran.

Yayin da aka titsiye su don jin wanda yayi musu ciki, sun sanar da su cewa mai ba fulawa ruwa ne. Hakan yasa mahaifiyarsu ta yanke jiki ta fadi kasa.

An samu bayanin yadda su ka fara lalata da shi gabadayansu ne bayan babbar ta kama ta biyun su na masha’ar. Daga nan ne ta bukaci itama ya biya mata bukatarta don ta rufa masa asiri.

Yayin da suke tsaka da lalata Riga kuma ta ukun ta kama su, itama ta nemi yayi lalatar da ita don ta rufa musu asiri.

Bayan daukar lokaci mai tsawo ana hakan, sai duk su ka samu ciki. A yanzu haka sun riga sun haihu. Kuma haka nan iyayen su ka yi hakuri bayan zurfafa tunanin saboda tsananin su ne hakan ya faru.

Iyayen sun kore shi daga aiki amma har yanzu ‘yan matan na tura masa kudi, su na kuma son sa a matsayin uban yaransu mata biyu da namiji daya.

Masu sauraranmu a Koda yaushe bayan Kun karanta wannan labarin zamu so karben a sahen mu na tsokaci.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button