
Subhanillahi Yadda Wani Ango Ya Mutu Bayan Kwana Biyu Daurin Auren Sa
Subhanillahi Yadda Wani Ango Ya Mutu Bayan Kwana Biyu Daurin Auren Sa
Wani ango da aka bayyana sunan shí da alhaji Kabiru Mai Magani Saminaka ya mutu bayan kwanaki biyu da daura auren sa akan hanyar sa ta dawowa Saminaka.
Angon ya mutu ne a sakamakon mummunan hadarin mota da faru dashi a yayin da yake komawa gida Saminaka, karamar hukumar Lere jihar Kaduna daga Pambeguwa, a jihar ta Kaduna, a ranar Litinin din da ta gabata.
Labarin mutuwar wannan sabon ango dai ya yadu cikin kankanin lokaci a kafafen sada zumunta na zamani musamman ma dai a kafar Faccbook inda ‘yan uwa da abokan arzikin mamacin suka dinga rubuta alhinin su da kuma addu’o’i.
Ance shima yaje wata gaisuwa ce ta mutuwa da aka yi a garin Pambeguwa dake jihar ta Kaduna a yayin da wannan hadarin ya same shi kan hanyar komawa.
Ance shima yaje wata gaisuwa ce ta mutuwa da aka yi a garin Pambeguwa
dake jihar ta Kaduna a yayin da wannan hadarin ya same shi kan hanyar komawa.
Wani mai suna Jamilu Suleiman Saminaka ya wallafa labarin mutuwar a shafin shi na Faccbook inda ya bayyana cewa kwana biyu kenan da kara auren Alhaji Kabiru Saminaka. Ya bayyana cewa ya mutu ne akan hanyar sa ta dawowa daga wajen wata ta’ aziyya da yaje Pambeguwa.
Kwanan shi biyu kenan da kara aure “Innalillai wa înna ilaihi rajiun. Bayan kwana biyu da karin Aurenshi Allah ya karbi rayuwarsa a hanyarsa tazuw ta’aziya Garin Pambegua.
Kwanan shi biyu kenan da kara aure
“Innalillai wa’inna ilaihi raji’un. Bayan kwana biyu da karin Aurenshi Allah ya karbi rayuwarsa a hanyarsa tazuwa ta aziya Garin Pambegua.
Allah yajilkan Alh Kabiru bilhakki Mai magani, ya karbi shahadarsa Alfarman Manzon Allah S. A. W Mukuma idan tamu tazo Allah yasa mucika da Imani” inji Jamilu Sulaiman.
Mutane da dama sunyi tsokaci na jimami gami da addu’o’i dangane da mutuwar wannan ango a hatsarin mota. Sun wallafa hotunan shagulgulan bikin wanda ba’a dade da yin shi ba.
Wani ma mai suna Abdullahi Usman Saminaka ya wallafa labarin gami da wallafa wani hoto na daga hotunan shagalin bikin, tare da yima mamacin addu’a.
“Inna-Lillahi-wa-Inna-Ilaihirrajiun Allah yayima Alhaji Kabiru mai magani Rasuwa. Allah yaji kanshi yasa ya huta ameen.”
“Innalillai wa’inna ilaihi rajiun. Bayan kwana biyu da karin Aurenshi Allah ya karbi rayuwarsa a hanyarsa tazuwa ta’aziya Garin Pambegua.
Allah yajikan Alh Kabiru Mai magani, ya karbi shahadarsa Alfarman Manzon Allah S. A. W. Mukuma idan tamu tazo Allah yasa mucika da Imani” inji wani Haruna Nuhu Saminaka.