Advertisement
Labaran Hausa

Subhanillahi Yadda Wani Matashi Dan Shekaru 18 Ya Kashe Mahaifiyarsa Don Takirashi Shege

Subhanillahi Yadda Wani Matashi Dan Shekaru 18 Ya Kashe Mahaifiyarsa Don Takirashi Shege

Wani matashi dan shekara 18 mai suna Tope Momoh ya shake mahaifiyarsa har sai da ta ce ga garinku saboda ta kira shi shege.

Tope ya amsa cewa ya halaka mahaifiyarsa mai suna Stella, makonni biyu bayan an birne ta, The Nation ta rahoto.

Bayyana sun nuna cewa ya aikata laifin ne a tsakar dare a ranar 6 ga watan Satumban 2022 a Ikakumi Akoko.

Tope, wanda aka gurfanar a gaban alkalin kotun majistare a Akure kan tuhumar kisar gilla, ya nemi a masa afuwa.

Mai gabatar da kara, Nelson Akintimehin, ya sanar da kotu cewa ba a san abin da ya yi sanadin mutuwar ta ba har sai da dan ya ce shi ya kashe ta.

Ya ce: “Momoh a yayin da ya ke bayani ga yan uwansa ya ce dole ta sa ya shake mahaifiyarsa har sai da ta mutu saboda ta tada shi a tsakar dare tana zaginsa tana ta kiransa shege.” Akintimehin ya ce laifin ya saba da sashi na 319(1) na kudin masu laifi Cap 37, Vol. II ta dokar Jihar Ondo, 2006.

Da aka bukaci ya yi magana, Tope ya ce: “Na kasa samun kwanciyar hankali a zuciya ta tun bayan da aka birne mahaifiyata. Hakan ya tilasta min fadin gaskiya cewa ni na shake ta ta mutu. Ina son kotu ta yi min sassauci.” Kotun ba ta amsa rokon Tope ba domin alkalin, Musa Al-Yunnus, ya bada umurnin a tsare shi a gidan gyaran hali na Olokuta. Al-Yunnus ya daga cigaba da sauraron karar zuwa ranar 20 ga watan Oktoba.

To Allah Ya Kyauta Masu sauraranmu a Koda yaushe bayan Kun karanta wannan labarin zamu so karben a sahen mu na tsokaci.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button