
Labaran Hausa
Subhanillahi Yadda Wata Yar Nijeriya Ta Mutu Yayin Da Likitoci Suke Tsaka Da Kara Mata Girman Mazaunanta A Indiya
Subhanillahi Yadda Wata Yar Nijeriya Ta Mutu Yayin Da Likitoci Suke Tsaka Da Kara Mata Girman Mazaunanta A Indiya
Wata ‘yar Najeriya mai shekaru 28 ta sheka lahira yayin da ta bazama kasar Indiya don a kara mata girman mazaunanta, Kamar Yadda LBI ta ruwaito.
Amelia Pounds ta tattara dukiyarta inda tace ba za ta zauna tana ganin mata na juyi yayin da ita kuma ta ke zaune ba, hakan yasa ta lallaba don likita ya kawo mata mafita.
An tattaro bayanai akan yadda ‘yar kasuwar ta rasa rayuwarta ana tsaka da aikin a wani asibiti wanda aka sakaya sunansa a cikin New Delhi, ranar Juma’a da safiyar 7 ga watan oktoban 2022.
Wata ma’abociya amfani da kafar sada zumuntar zamani ta Instagram, Vera Sidika ta tabbatar da aukuwar lamarin ta shafinta.
Subhanillahi Masu sauraranmu a Koda yaushe bayan Kun karanta wannan labarin zamu so karben a sahen mu na tsokaci.