
Sulaiman Isah wanda ya auri Baturiya ya bayyana yadda makiya suka sako su a gaba
Sulaiman Isah wanda ya auri Baturiya ya bayyana yadda makiya suka sako su a gaba
Wani dan jihar Kano mai shekaru 24 wanda ya auri Baturiya mai shekaru 48 ya bayyana yadda mahassada suka tasa shi gaba, inda suke fatan auren sa ya mutu, kamar yadda “Labarun Hausa” suka ruwaito.
A cewar Suleiman Isah, wanda ya auri dattijuwar Baturiyar nan mai suna “Janine Sanchez Reimann” akwai mutane da dama da suke jiran jin labarin auren su ya lalace.
Idan baku manta ba sun yi aure ne a ranar 13 ga watan Disamban 2020, a wuraren Gasau Panshekara dake cikin jihar Kano bayan haduwarsu a shafin sada zumunta na Instagram.
A cewar Sulaiman Isah, akwai mutane da dama dake ce masa ya ya dawo gida Kano da zarar auren ya lalace.
A cewarsa: Ina mamakin yadda mutane ke cemin da zarar batirina ya yi kasa wajibi ne in dawo Kano in zauna, kamar yadda ya wallafa a ranar Lahadi 25 ga watan Satumba
Mutane da dama sun yi masa tsokaci akan wallafar tasa, ga kadan daga ciki.
Shehu Sani ya yi masa tsokaci inda yace: Hassada kenan.
Inda shi kuma ya amsa masa da cewa: Wallahi kuwa Ranka shi dade basu da ilimi akan harkar komawa Amurka.
Babbo yace: Ka toshe su mana makiya ne tun daga zuciyarsu”
Rahoto daga👉 Labarun Hausa