
Tsabar Ha’intar Sa Da Budurwarsa Tayi Masa Yaji Cewar Da Yayi Aure Gwara Allah Ya Dauki Rayuwarsa
Tsabar Ha'intar Sa Da Budurwarsa Tayi Masa Yaji Cewar Da Yayi Aure Gwara Allah Ya Dauki Rayuwarsa
Wani matashin saurayi mai suna Seyi Oluleye da budurwa shi ta ha’inta ya fito ya shelanta wa duniya cewa shi da aure har abada, ba zai yi ba kwata-kwata.
Saurayin ya bayyana hakan ne a shafin shi na twitter a ranar Juma’ar data gabata, inda ya bayyana cewa ya gano cewa budurwa shi da yake shirin ya aura ta ha’ince shi, ya kamata tayi lalata da wani namiji daban.
“A yau ina son bayyana ma duniya cewa Ni Seyi Oluleye ba zan taɓa yin aure ba har abada. Ba zan taɓa ba. Nasan dangina zasu taru domin tattauna batun nawa, amma ko a jiki na. Bazan taɓa yin aure ba.” inji saurayin.
Yin wannan rubutu na shi keda wuya a shafin nashi na tuwita ne dai ya fara karɓar saƙuna da yawa daga ‘yan mata daban-daban, waɗanda yace sun rinƙa tambayar shi akan ko yana da muradin ya aure su.
Ya ce ya karɓi saƙonni daga kyawawan ‘yan mata sama da guda 100 bayan wancan rubutun nashi.
Saurayin ya ƙara da cewa kyawawan ‘yan mata sama da guda ɗari waɗanda bai taɓa tsammanin ma zai taɓa haɗuwa dasu ba sun biyo shi ta akwatun saƙon sa na tuwita suna yi mishi tayin aure.
Sai dai saurayin wato Seyi ya ce yana matuƙar godiya da saƙonnin nuna kulawa da ƙauna da ya samu daga ‘yan mata daban-daban. Ya kuma yaba da hankalinsu, kulawarsu da kuma basirar su.
Yace abun ne yayi matuƙar ƙona mishi rai, kuma yana cigaba da damun shi idan ya tuni cewa budurwar da yake so ya aura, wacce da ita ce ya so ya ƙare rayuwar shi, amma sai gashi ya kamata tana lalata da wani.
A dalilin haka ne ma ya yi rubutun, sannan kuma ya roƙi ubangiji da ya ɗauki rayuwar shi idan ya yi yunƙurin yin aure. “Idan kuma ma naji ina son yin auren, ina fatan Allah ya ɗauki rayuwata kafin lokacin auren.” inji saurayin.
Sai dai mutane da dama sunyi tsokaci akan rubutun na shi. Wasu sun tausaya mishi gami da bashi shawarar yayi haƙuri ya cigaba da tafiyar da rayuwar shi yadda ya kamata. Wasu kuma suma sun bada labarin makamancin irin hakan da ya faru dasu.
Masu sauraranmu a Koda yaushe bayan Kun karanta wannan labarin zamu so karben a sahen mu na tsokaci.