Advertisement
Labaran Hausa

Tsohuwar jarumar kannywood Wasila Isma’il tare da Mijinta sun cika shekaru 20 da auren su

Tsohuwar jarumar kannywood Wasila Isma'il tare da Mijinta sun cika shekaru 20 da auren su

Yayin da mutane da dama ke kallon auren jaruman Kannywood baya da dewa musamman idan aka kalli yadda aure ke ta mutuwa, jaruman na dawowa kan sana’ar su ta fim a wannan karon an samu mai karko.

Jaruma Wasila Isma’il wacce ta ja zarenta a masana’antar Kannywood a shekaru da dama da suka gabata ta cire tuta ita da mijinta “Al’amin Chiroma”, domin kuwa a ranar 6 ga watan Oktoba 2022 suka cika shekaru 20 cif da aure.

Chiroma mahaifi ne ga Lukman na
shirin fim din Labarina, mutane da dama sun dinga yi musu fatan alkhairi tare da addu’ar Allah ya kara musu dankon soyayya ya kuma sa mutuwa ce kadai zata raba su.

Rahoto daga👉 Labarun Hausa

Ga wasu daga cikin hotunan jarumar tare da mijinta da yaranta da Ubangiji ya azurta ta dasu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button