
Ummi Rahab matar Lilin Baba ta bayyana cewa tana dauke da juna biyu
Ummi Rahab matar Lilin Baba ta bayyana cewa tana dauke da juna biyu
Amaryar shahararren mawaki jarumi kuma furodusa a masana’antar Kannywood Shu’aibu Ahmed Abbas wanda aka fi sani da Lilin Baba, kuma tsohuwar jarumar Kannywood “Rahama Saleh Ahmed” wacce aka fi sani da UmmniRahab.
Ta sanar da cewa, ta samu juna biyu Ummi Rahab ta bayar da wannan sanarwar ne a Instagram, inda ta saka hoton ta sanye da wata jar atamfa, ta na zaune a kan kujera ta na murmushi, kamar yadda “Labarun Hausa” suka ruwaito.
A sakon da Ummi Rahab din ta fitar ta rubuta da manyan bakake cewa: Ina dauke da juna biyu.
Jarumar wacce ta bar fitowa a cikin finafinai tun bayan aurenta ta kuma yi kira ga masoyan ta da su taya ta murnar samun wannan abin arzikinda tayi, inda har ta yi alkawarin za ta bayar da tukwicin katin waya ga mutum 50 na farko da su ka tura sakon murnar a kasan hoton nata.
A kalamanta: Idan na samu ‘comments’ ta hanyar rubuta ‘Congratulations’ a karkashin wannan hoton, zan ba da kyautan kati ga mutane 50.
Sai dai ba ta fadi yawan katin da zata rabar ba a matsayin tukwicin ba, haka kuma amaryar ta Lilin Baba bata bayyana adadin yawan lokacin data kwashe tana dauke da juna biyunba.
Mutane da dama masu bibiyar ta a shafinta na sada zumunta instagram sun taya ta murna tare dayi mata fatan alheri.
Idan ba a manta ba dai anyi bikin Ummi Rahab da Lilin Baba a ranar Asabar, 18 ga watan Yuni 2022, a Tudun Murtala Kano, a kan sadaki N200,000.
Waliyyin ango jarumi Ali Nuhu, shine ya amsarwa Lilin Baba auren Ummi Rahab.