Labaran Hausa

Wace cuta ce ke damun tsohuwar jarumar kamnywood Fati Bararoji har ta koma haka

Wace cuta ce ke damun tsohuwar jarumar kamnywood Fati Bararoji har ta koma haka

Tun a safiyar ranar Asabar aka fara yada wadansu hotuna a a soshiyal midiya na jarumar Kannywood Fati Baffa Fagge wacce aka fi sani da Fati Bararoji, wadanda suka nuna Fatin tayi wata irin ramewa.

Ganin hotunan sai mutane suka dinga surutu akan ko dai tsohuwar jarumar tayi rashin lafilya ne, idan haka ne kuma wace irin cuta ce ke damun ta.

A binciken mujallar Fim ya nuna cewa, asali dai hotunan sun fara bayyana ne a shafin ita jarumar na TikTok da status, daga nan suka yadu zuwa sauran wasu shafukan na soshiyal midiya.

Mujallar Fim ta kira Fati Bararoji a waya domin tabbatar da halin da take ciki, sun tambaye ta ko tana da masaniya kan surutun da ya barke game da ita a soshiyal midiya.

Fati ta amsa da cewa, gaskiya nayi mamaki da naji mutane suna ta surutu a kan wannan hotunan, har ma ake cewa ba ni da lafiya to ni lafiya ta kalau ban yi rashin lafiya ba.

Abin dai da na sani cikin satin nan nayi tafiya zuwa Abuja daga nan sai na wuce Sokoto wajen taron biki, kuma ban huta ba na dawo Kano.

To wannan yanayi na tafiyar yasa ni gajiya duk ido na suka fada, kuma nazo na yi hotunan a haka shi yasa ake ganin kamar ba nida lafiya ko nayi wata rashin lafiya.

To gaskiya lafiya ta kalau kawai dai gajiyar tafiya ce Fakat.

Rahoto daga👉 Fim Magazine

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button