
Wani Al’amari Da Aka Gano Game Da Amaryar Da Dattijo Yayi Wuff Da Ita Da Ya Dauki Hankula A Kafar Sadarwa
Wani Al'amari Da Aka Gano Game Da Amaryar Da Dattijo Yayi Wuff Da Ita Da Ya Dauki Hankula A Kafar Sadarwa
An shiga cece-kuce a kafar sada zumunta a Najeriya biyo bayan ganin wani bidiyon da ya shahara na auren wani dattijo da matashiyar amaryasa.
‘Yan gulman kafar sada zumunta sun gaza hakuri, inda da yawa suke cewa amaryar ta yi kankanta da aure, wasu kuwa na cewa, ko da ma babba cewa, mijin nata ai ya zama kaka.
Sai dai, da alamu wannan amarya dai ba yarinya bace, kasancewar ta yiwu tana da kananan shekarun da gaske, amma dai ba ta yau bace.
Wasu na ta yada batun cewa, amaryar bata ma haura shekaru 12 ba, wasu kuma na kan ra’ayin a dai bincika a gano tushen batun.
A binciken da jaridar Aminiya tace ta yi, ta tattaro cewa, amaryar sunanta Sakina Musa Waziri, kuma ba kamar yarinya ce kamar yadda ake tsammani.
An gano cewa, wannan amarya shekaranta sun kai 21, kuma bazawara ce da shi wannan dattijon ya samu ya yi wuf da ita.
An kuma gano cewa, dattijon da ya angwance ba kowa bane face Dan Malikin Bauchi, Alhaji Aminu Muahmmad.
A cewar Aminiya, amaryar mai suna Sakina ‘yar asalin jihar Bauchi ce, an haife ta a Unguwar Railway da ta shahara a jihar.
Mahaifinta kuwa, wani tsohon alkali ne da ake kira Malam Musa Waziri, shi ma dan asalin jihar Bauchi ne.
Sakina ta shiga jami’ar jihar Bauchi da ke garin Gadau kafin ta yi amarcewar farko, inda aka ce auren bai dade ba ta rabu da mijin .
Yanzu dai Allah ya hada ta da mai girma Dan Maliki, an sha biki, an bar masu luguden lebe da maganganu a kafar sada zumunta.
Da Fatan Allah Ya Basu Zaman Lafiya.