Advertisement
Labaran Hausa

Wani dan Nageriya ya janyo tsaiko a hana jirgin sama tashi bayan yayi kashi a jirgin London zuwa Lagos

Wani dan Nageriya ya janyo tsaiko a hana jirgin sama tashi bayan yayi kashi a jirgin London zuwa Lagos

Wani jirgi da zai taso daga birnin Landan zuwa Legas ya samu tsaiko bayan da wani dan Najeriya da za’a mayar gida ya tuttuka kashi a ciki, bayan haka kuma ya bi duk ya yada kashin a cikin jirgin.

Wata a twitter mai amfani da @ImaniDH_ ta bayyana cewa, danuwanta yana cikin jirgin a yayin da lamarin ya faru, fasinjoji da dama basu ji dadin abin ba.

Tace, dan uwan na yana kan hanyar shi ta dawowa gida Najeriya ne daga Landan sai dai jirgin nasu ya samu tsaiko sakamakon kashi da wani dan Najeriya da jami’ai ke kan hanyar maidowa gida yayi, sannan ya yada kashin nashi ako ina a cikin jirgin.

Zlatan Ibile, shahararren mawaki dan Najeriya shima ya tabbatar da hakan inda yace, yana cikin jirgin shima.

Labarin gaskiya ne wani mai amfani da suna @Y_Etuhla twitter shima ya tabbatar da cewa labarin gaskiya ne, inda yace mutumin ya fito ne daga toilet ko wando babu.

A wani sako da ya karade kafar sada zumunta ta WhatsApp ance dan Najeriyan ya taho ne daga kasar Turkey ba tare da wasu gamsassun takardu ba.

Wannan ne dalilin da yasa hukumomin Landan din suka yi kokarin maido shi gida.

An hawo da shi kan jirgin daga nan sai ya kwabe wandon shi sannan ya kiba kashi a inda ake sanya abinci, daga nan kuma sai ya rika watsa kashin zuwa waje da bam-daban a cikin jirgin.

kamar yadda yazo a sakon, jami’ai sun kama dan Najeriyan sai da jami’an tsaro suka zu suka kama shi sannan kuma aka canja wa mutane jirgi.

Sakon ya kara da cewa, wannan lamari dai ya faru ne da jirgin Turai mai lamba BA 075, wanda yayi niyyar tashi da 11:20am na safe amma bai samu tashi ba sai zuwa 04:34pm na yamma.

Rahot daga👉 Labarun Hausa

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button