
Wani dan Nageriya yayi wuff da kyakkyawar Baturiya yadda har take dafa masa abinci
Wani dan Nageriya yayi wuff da kyakkyawar Baturiya yadda har take dafa masa abinci
Wani matashi dan Najeriya mai amfani da suna @kanorsamuel223 a manjajar TikTok, ya saka wani bidiyon budurwar sa Baturiya a kafar.
Wani bangare daga cikin bidiyon ya nuna kyakkyawar baturiyar na amfani da tukunyar gas tana soya masa filanten, ta nuna cewa lallai ita fa taga wurin zama.
ldan da ba domin yana yin kalar fatar jikinta ba, da sai ayi tunanin cewa ‘yar Najeriya ce bisa yadda ta gudanar da dafa abincin.
Mutane da dama sun yi tururuwar zuwa bangaren yin sharhi domin tambayar matashin yadda akayi ya samu wannan kyakkyawar baturiyar a matsayin budurwar sa.
Akwai akalla sama da mutum 400 da suka yi sharhi a kan bidiyon, yayin da sama da mutum dubu sha bakwai suka danna alamar so akan bidiyon.
Alex George ya rubuta: Pablo kayi kokari, lokacin ka ne na tunawa cewa lallai akwai so na gaskiya, ‘yan uwanta kar mu yasa nace maka nagode.
halo ya rubuta: Dan’uwa ya samu nasara a rayuwa, yoooooo000.
Dandy McCarthy ya ributa: Surkullenka mai karfi ne.
TikToker ya rubuta: Ya samu katin zama dan kasa.
washy ya rubuta: Har yanzu ina ta tunanin abinda za’a samar.
Rahoto daga👉 Labarun Hausa
Ga bidiyon a kasa domin ku kalla.