Labaran Hausa

Wani karamin yaro dan shekaru 7 ya rasa rayuwar sa sabida firgici bayan sojojin isra’ila sun biyo shi har gida

Wani karamin yaro dan shekaru 7 ya rasa rayuwar sa sabida firgici bayan sojojin isra'ila sun biyo shi har gida

Palasdinawa mazauna yankin West Bank sun yi jana’izar wani karamin yaro mai shekaru bakwai a duniya mai suna “Rayan Suleiman”, kamar yadda “Labarun Hausa” ta ruwaito.

Mahaifan yaron sun bayyana cewa, tsoron sojojin Isra’ila ne yayi sanadiyyar rasuwar sa, a jiya ne dai sojojin Isra’ila suka biyo Rayan Suleiman da shi da ‘yan uwansa suna tafiya daga gida zuwa makaranta.

Sun yi ikirarin cewa, sojojin sun buga musu kofa cikin fushi sannan sukayi musu barazanar kamu, Rayan wanda dan karamin cikin yaran uku ya rasu lokaci kadan bayan aukuwar lamarin.

Mohammed Suleiman, wani dan uwan Rayan ya shaidawa AlJazeera cewa, bayan Rayan ya dawo gida, sojojin sun biyo shi inda suke ta masa magana cikin fushi.

Sojojin sun yi masa magana cikin fushi
cewa, shi mai jefa dutse ne yayi kacibus da wani soja bayan ya ruga, lokacin da Rayan yaga sojan a gaban sa ya firgita kawai sai ya fadi kasa cikin tsoro.

Mahaifin Rayan mai suna “Yasser Sulaiman” ya bayyana cewa, Rayan ya fadi kasa ne bayan yaga sojojin Isra’ilan da suka biyo shi sun bayyana a gaban kofar sa.

Yayyen Rayan ‘yan shekara takwas da
shekara goma sojojin sun yi musu
barazanar kamu, Hatsaniyar da ake yi ce ta sanya Rayan ya sume.

Duk da kokarin da likitoci suka yi a asibitin Beit Jala, ba a samu an ceto rayuwar sa ba.

Rahoto daga👉 Labarun Hausa

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button