
Wani Lokacin Yan Iska Mazan Sun Fi Iya Soyayya Cewar Fatima Umar
Wani Lokacin Yan Iska Mazan Sun Fi Iya Soyayya Cewar Fatima Umar
Wata budurwa ma’abociya amfani da kafar sada zumuntar zamani ta Twitter mai suna Fatima Umar ta bayyana irin mazan da su ka fi iya Soyayya.
Yayin da mata da dama ke neman maza natsatstsu da hankali, ita ra’ayinta dangane da maza wadanda su ka fi lakantar soyayya.
Budurwar wacce tayi wallafar tare da hadawa da wani hotonta wanda ta dau kyau, ta bayyana cewa maza yan iska sun fi iya soyayya
A cewar F’atima, wani lokacin maza yan iska sun fi iya soyayya maimakon maza masu natsuwa Kamar yadda ta wallafa:
“Wani lokacin ‘yan iskan maza sun fi ya soyayya.”Tabbas wannan wallafar ta dauki hankali kwarai, inda wasu ke ganin gaskiya maganarta, wasu kuma na ganin akasin haka.
Masu sauraranmu a Koda yaushe bayan Kun karanta wannan labarin zamu so karben ra’ayoyinku a sahen mu na tsokaci.