Advertisement
Labaran Hausa

Wani magidanci da yake lalata da ‘yayan sa Mata har biyu bayan rabuwarsa da Mahaifiyar su asirin sa ya tonu

Wani magidanci da yake lalata da 'yayan sa Mata har biyu bayan rabuwarsa da Mahaifiyar su asirin sa ya tonu

Wani magidanci da yayi ta cigaba da yin lalata da ‘yayan shi ‘yan mata su biyu tun bayan rabuwa da yayi da mahaifiyar su wani lokaci can baya.

Hausaloaded na ruwaito cewa, Yara ne ‘yan mata su biyu Kwamishiniyar walwala da jin dadin mata ta jihar Anambra tace an kama wani magidanci mai suna “Nwobi” mai matsakaitan shekaru bisa tuhumar cewa, yana lalata da yayan shi mata su biyu da mai shekara uku da kuma ‘yar shekara biyar.

Ma’aikatar walwala da jin dadin matan ce dai tare da hadin gwuiwar jami’an tsaro na sibil difens suka yi nasarar cafke mutumin.

Sun gudanar da samame ne kan mutumin a ranar Laraba 19 ga watan Oktoban nan da muke ciki, ance mutumin dai sun rabu da matar ta shi tun wani lokaci a shekarar 2020, kamar yadda dai majiyar mu ta Punch ta ruvwaito.

Da aka ji ta bakin yaran sun tabbatar da cewa, mahaifin nasu yana lalata da su, kuma su basu sha’awar kara komawa gidan nashi domin gudun abinda kan iya zuwa ya dawo.

Sai dai kuma wanda ake tuhuma ya musanta zargin inda yace, baya da masaniya akan cewa wani yana yin lalata da ‘yayan shi ballantana kuma ace shi karan kanshi.

Yasha alwashin daukar mummunan mataki akan wanda yazo ya kawo karar shi kan hakan.

Rahoto daga👉 Hausaloaded

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button