Advertisement
Labaran Hausa

Wani Magidanci ya bayyana yadda Matarsa take masa kunzugu idan zai kwanta don kada yayi fitsarin kwance

Wani Magidanci ya bayyana yadda Matarsa take masa kunzugu idan zai kwanta don kada yayi fitsarin kwance

William Getumbe, fitaccen mawakiny abon addinin kirista ya bayyana cewa, yana yin fitsarin kwance idan har ya kwanta bacci, da kuma yadda yake dawainiya da lalurar, kamar yadda “Labarun Hausa” suka ruwaito.

Yayin tattaunawar da suka yi da Jaridar Kenya ta TUKO.co.ke, mawakin ya bayyana cewa, matarsa Virginia Masitha ta san halin da yake ciki sannan ita ce ma take yi masa kunzugu ko wanne dare kafin su kwanta.

Lalurar fitsarin kwance ba sabuwarlalura bace kuma tana faruwa da zararmutum ya kwanta yana bacci ba tareda sani ba ya fara fitsari. A cewarGetumbe, akwai manya da dama da kefitsarin kwance amma su na jin kunyarbayyana wa duniya.

Yace, hakan ya yi matukar raba auren jama’a da dama, mawakin yabon Yesun ya yaba wa matarsa akan kokarin da take yi dangane da shi da lalurarsa inda take ji da shi tamkar jariri ako wanne dare.

Akwai aure da dama da ya mutu sabida fitsarin kwance, sai dai matata ta fahimceni fiye da tunani inda take yimin kunzugu ako wanne dare ba tare da raina ni ba, inji shi.

Getumbe ya shawarci duk masu lalurar fitsarin kwance musamman maza masu iyalin da su dinga yin kunzugu kafin su kwanta domin gudun yin shi a gado.

Ya cigaba da cewa: Akwai maza da dama dake amfani da kunzugu kamar masu zuwa makaranta, ‘yan giya da sauran marasa lafiya.

Ina shawartar maza da kada su guji kunzugu don tsaftace dakin kwanansu, a cewar Getumbe.

Rahoto daga👉 Labarun Hausa

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button